You are here: HomeAfricaBBC2023 11 19Article 1883948

BBC Hausa of Sunday, 19 November 2023

Source: BBC

Yadda daruruwan mutane ke ficewa daga asibitin al- Shifa da ke Gaza

Yan gudun hijira Yan gudun hijira

Daruruwan mutane ciki har da wasu marasa lafiya sun fice daga babban asibitin zirin Gaza a ranar Asabar. Wasu ma’aikatan lafiya sun ce an fada mu su cewa su bar asibitin amma Israila ta musanta hakan.

An dai ga mutane da dama suna tafiya a kan titunan da ke cike da baraguzan gine- ginen da suka ruguje yayin da ake ta harbe-harbe.

A wani labarin kuma jami'an ma'aikatar kiwon lafiya ta kungiyar Hamas sun ce wasu abubuwa masu fashewa biyu sun yi sanadin mutuwar mutane 80 a Jabalia da ke arewacin Gaza.

Israila ta shaida wa BBC cewa ba za ta iya tabbatar da cewa ta kai hari kan wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya da mutane ke amfani da ita domin samun mafaka ba .

Sai dai ta ce tana gudanar da bincike.

Sai dai ta ce tana gudanar da bincike.

Sashin tabbatar da sahihancin labarai na BBC ya bi didigin wani hoton bidiyo na makarantar al Fakhoura da ke Jabalia wanda ya nuna mutane da dama ciki har da mata da yara wadanda suka samu munanan raunuka ko kuma kwance a kasa babu motsi a sassa daban-daban na ginin.

Akwai mutane fiye da 20 da alamarin ya rutsa da su a cikin hoton bidiyon kuma rabi daga ciki suna cikin wani daki da ke kasan ginin wanda ya nuna alamun barna sosai.

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu, Philippe Lazzani ya ce ya ga hotuna masu tayar da hankali da mutane da dama da aka kashe da kuma wadanda aka raunata a daya daga cikin makarantun da ke karkashin kulawar hukumarsa inda “dubban mutane da suka rasa muhalansu ke samun mafaka” “Wadanan hare hare ba za su zama ruwan dare gama gari ba, ya zama dole a daina,”in ji shi

A gefe daya kuma, ma’aikatar lafiya ta kungiyar Hamas ta ce an kashe mutane fiye da 30 daga gida daya a yakin Jabalia, a abinda ta kira harin Israila.

Rundunar sojin Israila ba ta ce komai kan rahoton ba amma ta ce tana fadada farmakinta a Gaza ciki harda Jabalia domin ta kai wa Hamas hari

Ma’aikatar kiwon lafiya da ke karkashin ikon Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe a Gaza ya kai 12,300. Ana fargabar cewa fiye da dubu 2000 na karkashin baraguzan gine- ginen da suka ruguje.

A asibitin al-shifa, wani dan jarida ya shaida wa BBC cewa, “marasa lafiya da ba za su iya tafiya ba da likitoci kalilan ne suka rage”

" Mun daga hanunmu kuma mun dauki fararen tutoci," in ji Khader, wanda ya ziyarci asibitin na al-Shifa.

Tun farko, ma’aikatar kiwon lafiya ta Hamas ta ce marasa lafiya 120 ne suka rage a cikin asibitn da kuma jarirai bakwaini da ba a san adadinsu ba

Rundunar sojin Israila ta musanta cewa ta bada umarnin kwashe marasa lafiya daga aibitin al -Shifa kuma ta ce ta amince da bukatar da darektan asibitin da ya shafi wadanda suke son su fice a ba su damar yin haka ba tare da an kai mu su hari ba.

Dr Ramez Radwan, wanda likita ne da ya ce mahukuntan Israila sun umurce shi ya fice daga asibitiin ya bayana halin “ukkuba” da mutane suke ciki, yana mai cewa babu magungunan rage radadin ciwo ko na kashe kwayar cuta kuma wasu daga cikin marasa lafiya “ tsutsotsi sun fara fita daga ciwon da suka ji”

Sojojin Israila sun kai wa samame asibitin a cikin ‘yan kwanakin nan, a wani bangare na abinda suka kira hari kan Hamas amma har yanzu sun kasa bayar da kwararan hujjoji da suka nuna cewa mayakan Hamas na aiki karkashin asibitin

Sun fadawa Falasdinawa da ke arewacin Gaza da su fice domin tabbatar da tsaron lafiyarsu, a yanzu sun fara fadawa mutanen da ke Khan Younis a kudancin Gaza inda dubban mutane da ke Gaza da suka tsere ke samun mafaka da su fice daga wurin.