You are here: HomeAfricaBBC2023 11 19Article 1883924

BBC Hausa of Sunday, 19 November 2023

Source: BBC

Yadda ciwon rabuwa da masoyi zai amfani lafiyarku

Hoton alama Hoton alama

Ko akwai wani alfanu a rabuwa da masoyi? Ƙila za ku yi mamaki game da wannan tambaya cewa ko akwai wanda zai yi murna da rabuwa da masoyinsa kuwa, ballantana ma a yi tunanin amfanin hakan.

Rosie Wilby, marubuciyar littafin 'The Breakup Monologues', na ganin alfanu mai yawa game da rabuwa da masoyi ko masoyiya - wato dai 'break up' a Turance.

Rosie na gabatar da shirye-shirye ta manhajar Podcast game da zamantakewar al'umma da kuma soyayya.

Daga baya ta sake rubuta wani littafin da irin wannan sunan. A littafin, ta yi magana kan rayuwarta. Bugu da ƙari, duk abin da ta fahimta game da alaƙa tsakanin mace da namiji a lokacin da take hira da baƙi a shirin nata, sai ta zuba su a littafin.

Ta kuma tattauna da likitoci, da masana zamantakewa, da masana kimiyya kafin ta rubuta littafin.

Ta faɗa wa BBC Rail cewa muna iya koyar abubuwa da yawa game da rabuwa da masoyi, tana mai cewa ba abu ne da ake kallo a matsayin mai kyau ba.

Damar fahimtar halayenka

Rosie Wilby, na ganin cewa rabuwa da masoyi zai bayar damar sake tunani kan mutumin da ya kamata mu yi soyayya da shi, a wasu lokutan kuma hakan na faruwa ne kawai ta hanyar zafin rabuwa da masoyi.

Muna bayan ingantattun bayanai game da kawunanmu, kuma za su taimaka mana wajen ɗaukar matakan da suka dace. Dakta Sameer Malhotra, masanin lafiyar kwakwalwa da ɗabi'ar ɗan'adam ya ce a wasu lokuta rabuwa da masoya na bayar da dama wajen buɗe idanu.

"A wasu lokuta rabuwa da masoyi zai sa ka ƙara samun ƙarin fahimtar abubuwa," in ji shi.

Daga nan sai ka gyara kura-kuran da ka aikata, ya danganta ga yadda ka ɗauki rabuwa da masoyi. Idan ka riƙa ɗora alhakin da masoyinka, ba za taɓa ƙoƙarin gyara wa kanka ba.

Kowa akwai yadda nasa lamarin ya kasance

Shivani Mishrisadhu ƙwararriya kan ilimin halayyar ɗan'adam a birnin Delhi, ta ce rabuwa da masoyi abu ne mai wahala ga kowa, sai dai kowa da yadda nasa lamarin ya kasance, saɓanin wasu.

Yayin da take hira da BBC, Shivani Mishri Sadhu ta ce a wasu lokuta rabuwa da masoyi ka iya zama wani darasi a garemu.

'Idan kuka rabu da masoyanku, Ka samu damar fahimtar kanka da kuma yadda za ka inganta tunaninka, In ji ta.

"Dole kuma mu amince cewa mun yi kuskure a soyayyarmu''.

Kwatanta rabuwa da masoyi da jarabtuwa da shan kwaya

Rosie Wilby ya kwatanta zafin rabuwa da masoyi d ajarabtuwa da shan ƙwaya

A fahimtarsa, dbi'ar mutum bayan rabuwa da da masoyi ta yi kama ɗabi'ar mutumin da ya jarabtu da shan ƙwaya idan ya daina.

Dakta Sameer Malhotra ya kuma ce idan sinadarin soyayya, wato oxytocin hormone kan ƙaru a ƙwaƙwalwa, musamman idan akwai wanda kake soyayya da shi.

Hakan na faruwa a kowace iriyar soyayya. "A lokuta da dama hakan na sa ƙwaƙwalwa ta riƙa tunanin masoyi," in ji shi.

Zai sa ka riƙa jin kodayaushe kana son haɗuwa da mutumin da kake, amma idan aka samu rabuwa da masoyi ko sinarar suka daina aiki, sai mu zamu tamkar mutanen da suka jarabtu da shan ƙwaya, idan ba su sha ƙwayar ba.

Shin za a iya gaggauta ƙulla wata soyayyar?

Soyayya wata aba ce da jima a rainonta, in ji Rosie Wilby. Wannan aiki ne mai matuƙar wahala, saboda soyayya aba ce marar tabbas.

"Ya kamata ka nazarci wasu mutanen ta hanyar la'akari da kyawawa da munanan halayensu, Yana da matuƙar muhimmanci ka ɗauki lokaci ka nazarci kanka kafin ka koma wata soyayyar", In ji Rosie Wilby.

Amma ba wai ka ƙebe kanka kai kaɗai ka ce ba za ka sake yin soyaya ba.

Kula da kanka na da matuƙar muhimmanci

Dakta Sameer Malhotra ya ce a lokuta da dama mutane kan yi tunanin cewa ya kamata su gaggauta ƙulla wata soyayyar da zarar sun rabu da masoyansu. Sai dai ba hakan ne ya kamata ba.

Babbar soyayya, ita ce kula da kanka, ya kamata ka samu wasu dokoki da ƙa'idoji, ka samu nutsuwa da juriya.

Dakta Malhotra, ya ce ya kamata ka yi amfani da ƙarfi, da tunaninka wajen samar wa kanka wasu abubuwan da za su ɗauke maka hankali.

Ya ce ya kamata mutum ya yi ƙoƙarin fahimtar kansa a soyayya, sannan ya yi ƙoƙarin cire matsalolinsa bayan ya fahimce su.

Dr. Malhotra ya ce kada mu yi wa wani magana, ko mu nuna zaƙuwarmu cewa dole sai mun yi samu abokin ƙulla sabuwar soyayya.

"A duk lokacin da muka yi magana a kan soyayya, ya kamata mu yi la'akari da abu guda biyu, kula da lafiyarmu, da sama wa kanmu lafiya", in ji shi, a taƙaice dai shi ne kula da soyayyar na da matuƙar muhimmanci.

A kodayaushe ku zama kuna sane da halin da junanku ke ciki, haka kuma a lokaci guda ya kama ku riƙa bai wa kanku 'yar tazara, saboda kowa na da wasu abubuwan da suka shafe shi shi kaɗai.

Sauyawar ɗabi'ar mutane

Shivani Mishri Sadhu ta yi imanin cewa a kudancin yankin Asiya, tunanin mutane kan rabuwa da masoya ya fara sauya wa.

Masana na cewa a yanzu mutane sun fara fahimtar cewa shiga tsanani a soyayya na wahalar da lafiyar jikinsu da ta ƙwaƙwalwa da zuciyarsu, to amma yanayin a nan ya kai matakin da ba za ka iya barinsa ba.

Pooja Shivam Jaitley na ganin cewa abin da ya kamata mutum ya yi bayan rabuwa da masoyi shi ne ƙulla alaƙa da wasu mutanen".

"Sannan ka fara yin abubuwan da za su riƙa ɗauke maka kewa domin inganta lafiyarka, haka kuma ka koyi yadda za ka rayu ba tare da kowa ba, idan ka yi haka, haƙiƙa zai sa farin cikinka ya dawo bayan zafin rabuwa da masoyi", In ji Shivani Mishri Sadhu.