You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837748

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Yadda bashi ya yi wa jarumi Sunny Deol katutu

Sunny Deol, Fitaccen jarumin fina-finan Indiya,  kuma ɗan majalisar a jami'iyyar BJP Sunny Deol, Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, kuma ɗan majalisar a jami'iyyar BJP

An shiga cikin wani yanayi na ce-ce-kuce kan Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, kuma ɗan majalisar a jami'iyyar BJP Sunny Deol.

Muhawarar da ake tafkawa kan Jarumin ba ta tsaya kaɗai a kan nasararsa ta fim din Gadar-2 ba, akwai batun dimbin bashin da bankin Baroda ke bin sa, abin da ya kai ga ana kokarin gwanjon wani gidansa da ke Mumbai.

Bankin ya ce tun daga watan Disambar 2022, ɗan majalisar da ke wakiltar Gurdaspur, Sunny Deol ya gaza cimma wa'adin biyan bashin milyoyin kuɗaɗe da ya karɓa rance daga bankin Baroda, don haka aka yanke hukuncin yin gwanjon gidansa da ya bayar a matsayin jingina.

A ranar 19 ga watan Agusta, lokacin da aka buga wannan sanarwar a jaridu, mutane sun fara yiwa Sunny Deol tambayoyi masu alaƙa da rashin biyansa bashin.

Ya ki cewa komai, yana mai cewa al'amarin sirri ne. Sai dai kuma, bayan kwana biyu, bankin Baroda ya janye wannan sanarwar saboda wasu dalilai na na'urar fasaha.

Abin tambaya anan shine me yasa bankin yayi haka? Shin Sunny Deol ya shirya biyan bashin ne? Akwai wani matsin lamba akan bankin? Menene girman dalilan da bankin ya bayar?

Jarumi Sunny Deol ya karbi lamuni daga bankin Baroda domin gina gidansa mai suna Sunny Villa dake Mumbai.

Dan uwansa Bobby Deol da mahaifinsa Dharmendra Singh ne suka taimaka masa wajen samun rancen kuɗin.

Sannan, kadaorin da ya bada jingina a wajen karɓan rancen har da wani kamfaninsa 'Sunny Sound Pvt Ltd.

Wata sanara da aka wallafa a wani shafi da ke kwarmata labarin halasta kuɗaɗen haram, na cewa Sunny Deol ya karɓi wannan rance ne a shekarar 2016 don daukar nauyin fim.

A cikin takardar rantsuwa da aka bai wa hukumar zaɓe a lokacin zaɓen Lok Sabha na 2019, Sunny Deol ya ambaci cewa ya karbi lamuni na Rs 50 crore.

Sakamakon rashin biyan bashin, bankin ya ayyana shi a matsayin wani kadara mara amfani.

Bankin Baroda ya yanke shawarar siyar da gidan Sunny Deol wanda ya bada jingina domin ya mayar da kuɗinsa.

Bankin ya fitar da sanarwar da aka buga a jaridu da dama a ranar 19 ga Agusta, 2023, inda ya bayyana cewa yana bin Sunny Deol bashin kuɗaɗen da suka kai har Rs 56 crore da kuma kuɗin ruwa da ya karu daga Disamba 2022, kuma domin dawo da kuɗaɗe ya yanke hukuncin yin gwanjon gidansa da ake kira villa Sunny Deol.

An kiyasata cewa za a yi gwanjon gidan a kan miliyan 51 zuwa 43 na kuɗin kasar, a ranar 25 ga Satumba, 2023.

Bankin ya bukaci masu sha'awar sayen gida da su mika tayinsu ta shafinsu, kuma mutum na da damar saka kashi 10 ckin 100 na farashin da ake bukata.

An kuma ce masu sha'awar saye za su iya zuwa su gani a ranar 14 ga Satumba.

Sai dai kuma Bayan kwana biyu bankin ya janye sanarwar yin gwanjon gidan Sunny Deol.

Bankin ya fitar da wata sanarwa mai dauke da dalilai uku da suka haddasa hakan. Dalili na farko shi ne cewa bankin ba shi da cikakkun bayanai game da mayar da kuɗin.

Keshav Khaneja, wanda ya rike manyan mukamai da dama a reshen kula da karbo kadarori na bankin kasuwanci na Oriental, ya nemi karin haske akan bayanin bankin.

Wani dalili da Bankin Baroda ya bayar na janye sanarwar shi ne sanarwar sayar da kadarorin ta dogara ne akan mallakar kadarorin.

A ranar 1 ga watan Agusta ne bankin ya mika takardar neman mallaka ga babban kotun yankin, wanda ke jiran amsa.

Dalili na uku kuma mafi muhimmanci da Bankin Baroda ya bayar shi ne, bayan da aka buga sanarwar sayar da su Sunny Deol ya tuntube su domin daidaita biyan bashin.

Ashwini Rana, kwararre kan harkokin banki kuma wanda ya kafa dokokin Bankin, ya ce, "Idan mutum ya biya bashin a cikin kwanaki 30 bayan an buga sanarwar siyar da shi, bankin na iya janye sanarwar."

To abin tambaya shine shin Sunny Deol ya biya bashin Rs 56 crore da bankin ke binsa? A wannan lokacin, bankin bai bayar da amsar wannan tambayar ba.