BBC Hausa of Monday, 20 February 2023

Source: BBC

Yadda ake cin zarafin matan da ke aiki a gonakin ganyen shayi a Kenya

Shayin Kenya Shayin Kenya

An gano yadda ake cin zarafin matan da ke aiki a manyan gonakin ganyen shayin Kenya da ke samar da ganye shaye ga manyan kamfanonin a Birtaniya da suka haɗa da PG Tips da Lipton da kuma kamfanin Sainsbury.

Fiye da mata 70 ne suka shaida wa BBC cewa masu lura da gonakin ganyen shayin da suke aiki mallakin kamfanonin Birtaniya, sun ci zarafinsu.

Wasu hotunan bidiyo da aka ɗauka a asirce sun nuna masu lura da gonakin kamfanonin Unilever da James Finlay & Co, suna tilasta wa matan da suka je neman aiki yin lalata da su kafin su ba su aikin.

Kawo yanzu an kori manajojin gonaki guda uku.

Kamfanin Unilever ya fuskanci makamancin waɗannan zarge-zarge fiye da shekara 10 da suka gabata.

Kuma ya ƙaddamar da dokar ba sani-ba-sabo kan duka mutanen da aka kama da laifin cin zarafin mata a kamfanin.

To sai dai wani binciken haɗin gwiwa tsakanin sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye, da na Panorama ya gano cewa ba a ɗauki matakai kan laifukan cin zarafi ba.

Wakilin BBC ya zanta da wasu mata da ke aiki a gonakin ganyen shayi mallakar kamfanonin biyu.

Kuma wasu da yawa sun shaida masa cewa kasancewar samun aiki na da matuƙar wahala, ba su da zaɓi, dole su yadda jagororin gonakin su yi lalata da su domin ba su aiki don su dogara da kansu.

"Ba zan iya rasa aikina ba, saboda ina da ƙananan yara," kamar yadda wata mace ta bayyana.

Wata matar ta shaida wa BBC cewa wani ƙaramin manaja ya dakatar da ita daga aiki, har sai da ta yadda ya yi lalata da ita, sannan ya mayar da ita bakin aikinta.

"Cutarwa da zalunci ne, sai ya yi lalata da ke, sannan ya ba ki aiki,'' in ji ta.

Wata matar kuma ta faɗa wa BBC cewa mai lura da gonar da take aiki ya sanya mata cutar HIV bayan da ya tilasta mata yin lalata da shi.

Domin samun gamsassun hujjoji kan zarge-zargen cin zarafin mata da ake yi a gonakin, BBC ta ɗauki Katy (ba sunanta ne na aihini ba) da ta yi shigar-burtu a matsayin wadda ta je neman aiki gonakin.

Da farko an gayyaci Katy zuwa tantance neman ma'aika a kamfanin James Finlay & Co called John Chebochok.

Da fari an sauya wajen gudanar da tantancewar zuwa wani ɗaki a Otal.

Mista Chebochok -wanda ya shafe sama da shekara 30 yana aiki a gonakin Finlay - shi ne mutumin da matan da BBC ta zanta da su, suka fi ambata a matsayin wanda ya fi cin zarafinsu.

Mista Chebochok ya yi ƙoƙarin janyo Katy zuwa kusurwar ɗakin, sannan ya umarce ta da ta cire kayanta sannan ta rungume shi.

"Zan ba ki wasu kuɗi, sannan zan ɗauke ki aiki. Kin ga na taimake ki, to ke ma ki taimaka min,'' in ji shi.

''Mu yi sauri, mu gama mu tashi, sai ki dawo ki kama aiki''.

Katy ta nuna masa cewa ba za ta amince da buƙatarsa ba. Da ya ga alamar ba za ta yadda ba sai ya haƙura, daga nan ne kuma ɗaya daga cikin ma'aikatan da ke aikin binciken ƙwaƙwaf tare daKaty -wanda aka ajiye a kusa da wajen domin ya kareta - sai ya kirata a waya, kiran da ya ba ta damar sulalewa daga ɗakin.

''Na yi matuƙar tsorata, na kaɗu sosai. Lallai matan da ke aiki tare da Mista Chebochok na fuskantar cin zarafi,'' in ji Katy.

Kamfanin James Finlay & Co ya ce tuni ya kori Mista Chebochok, bayan da BBC ta tuntuɓi kamfanin.

Kamfanin ya kuma ce ya kai rahotonsa wajen 'yan sanda waɗanda a yanzu suke gudanar da bincike game da lamarin cin zarafin mata musamman a reshen kamfanin da ke Kenya.

Haka kuma Katy ta fuskanci wani cin zarafi a lokacin da take gudanar da binciken sirrin a wata gona da kamfanin Unilever ke gudanarwa.

An gayyace ta zuwa bikin ƙaddamar da sababbin ma'aikata wanda manajan kamfanin mai suna Jeremiah Koskei ya yi jawabi ga sababbin ma'aikatan kan tsarin kamfanin na ba-sani-ba-sabo ga waɗanda aka kama da laifin cin zarafin mata.

Bayan kammala jawabin nasa ne kuma, sai mai dokar bacci ya ɓuge da gangyaɗi, domin kuwa ya umarci 'Katy' da ta same shi a wata mashaya a wani otal da maraicen wannan rana, inda ya yi ƙoƙarin tursasa mata yin lalata da shi - inda ya ce mata za su koma gidansa su kwana tare.

Daga baya Katy ta ce: "Da a ce da wannan damar kawai na dogara, da ban san yadda rayuwata za ta ƙare ba.

An sanya Katy cikin tawagar masu cirar ciyawa a gonar, aiki ne mai matuƙar wahala, kwanaki shida ake a cikin mako, kuma mata da yawa kan nemi a sauya musu wannan aikin.

Wanda ke lura da aikin, mai suna Samuel Yebei, ya nemi yin lalata da ita domin sauya mata aiki mai sauki a gonar.

A lokacin da Katy ta kai rohoton ɗabi'ar cin zarafin mata da manyan ma'aikatan Unilever ke aikatawa ga ɗaya daga cikin jagororin kamfanin, ya faɗa mata cewa ''Ki tsaya a kan ƙudurinki, kar ki yadda ki bayar da kanki don neman aiki.''

Duk da bibiyar da ta yi domin jin irin matakin da aka ɗauka kan waɗanda suka ci zarafinta, ba ta samu bayanin komai ba.

Kamfanin Unilever ya ce ya yi matuƙar ''kaɗuwa da bakin ciki'' bisa waɗannan zarge-zarge.

Kamfanin ya sayar da reshensa na Kenya a lokacin da BBC ke tsaka da naɗar hotunan bidiyon sirri.

Sabon mai kamfanin reshen mai suna 'Lipton Teas and Infusions' ya ce ya gaggauta korar manajojin kamfanin biyu, tare da bayar da umarnin gudanar da ''cikakken bincike game da zarge-zargen.