You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837766

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Yadda ake amfani da fitsari don gane mai ciki fiye da shekara 4,000

Hoton alama Hoton alama

A wannan zamani gane mace mai ciki abu ne mai sauƙin gaske: da an yi amfani da 'yar ƙaramar na'urar da ke hoton sama, kai-tsaye za ta nuna idan har mace na da juna biyu - wasu layuka biyu za su bayyana domin tabbatar da idan da juna cikin ko akasin haka.

An soma amfani da wannan dubarar gwajin ciki a gida tun a shekarar 1960.

Waɗannan na'urorin na iya gano wani sinadarin gonadotropin da mahaifa kan fitar da galibin sa idan mace na da juna biyu wanda kuma ake samun sa cikin fitsari.

Idan kuma aka yi amfani da gwajin jini domin gano ko akwai juna biyu, ya kan ɗauki kimanin kwana 11 ne saɓanin idan aka yi gwajin fitsari, shi kam ya kan ɗauki 'yan kwanaki ne kawai a samu sakamakon.

Daga soma gudanar da binciken sakamakon zai soma bayyana. Amma abubuwa sun sha bamban a wancan lokaci. Ɗaukewar al'ada da kuma rashin son cin abinci ko jin ƙarfin jiki na iya zama manyan alamomin da ke nuna mace na da ciki.

Amma kuma sai daga baya aka ƙara gano cewa ba dole sai da juna biyu ne kawai ake samun waɗannan alamomi da aka ambata ba, ya iya zama wata cuta ce ta daban.

Tun a zamanin tsohuwar daular Girkawa ake cewa wai mata na iya fahimtar idan har sun samu juna biyu bayan sun sadu da mazajensu, wanda sam babu gaskiya a wannan magana.

Hasali ma dai samun ciki ba abu ne da za iya ganewa da wuri daga yin jima'i ba. Amma wannan fa bai hana mutane amfani da wasu hanoyin tantance idan har suna da juna baiyu ba, kuma suna da asiri sosai.

Mujallar "Aphorisms" ta masanin ilmin likitancin nan Hippocrates, da aka wallafa a ƙarni na 4 ta bayar da shawarar cewa idan mace na buƙatar samun ciki to ta sha barasar da aka garwaya da ruwa da zuma kafin kwanciyar aure, wai hakan zai sa cikinta ya kumbura har ma ya rinƙa wani ƙugi.

Wani mai koyar da ilmin tarihi a Jami'ar Auckland, mai suna Kim Phillips, ya bayyana a cikin wata muƙala mai suna, " Sirrin Mata", wadda ta bayyana wani binciken kiyyon lafiya da a aka gudanar a ƙarni na 13 da ya ba jama'a shawarar cewa wai idan har nonuwan budurwa suka rusuna, to alamu ne na tana ɗauke da juna biyu.

Wai wannan a cewar hasashen, duk lokacin da ɗan tayi ya soma girma a cikin mahaifa, to jinin al'ada kan canza hanya inda zai ci gaba da bi kai taye zuwa nonuwa saɓanin yadda aka saba.

To amma a wannan lokaci da muke ciki, fitsari ya zama wata hanyar da ake amfani da ita wajen samun gamsasshiyar amsar idan har mace na da juna biyu. Duk da yake ana yi wa sabuwar dubarar kallon ta zamani, amma an jima da sanin ta dubban shekru da suka gabata.

Hasalima dai, fiye da shekara 4,500 da suka wuce Malaman Misirawa sun bayyana cewa ana amfani da gwajin fitsari domin tabbatar da idan mace na da ciki.

Daga cikin rubuce-rubucen da suka yi kan wannan akwai cewar wai idan mace ta yi fitsari saman tsabar alkama ko sha'ir na tsawon kwanaki to ana iya ganewa muddin tana da ciki.

Idan har sha'ir ɗin ya tsiro to akwai yuwar tana ɗauke da cikin ɗa namiji amma idan har alkama ce ta fito babu tantama mace za a haifa.

Amma kuma idan har babu wani daga cikin su da ya tsiro hakan na nufin macen ba ta ɗauke da juna biyu kenan. A ƙarni na 16, ba a fassara kalmar "allura" daidai wadda a harshe irin na turancin Ingilshi ana fassara ta da sunan da aka san ta da shi wato, "allura" amma sai ake kiran ta "attura".

Wannan ma ya sa ake da wata al'ada wadda wai da dare mace za ta saka allura a cikin fitsarinta zuwa wayewar gari sai ta duba ta gai. Idan ta ga launinsa ya canza to wannan wai alama ce mai nuna tana ɗauke da juna biyu.

A na iya gudanar da duk waɗannan gwaje-gwajen ba tare da kulawar likita ba. Tun lokacin da aka kafa Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Landan a shekarar 1518, al'adar ƙyamar zamani ta ƙaru, inda ta hana mata shiga koyon aikin kiyyon lafiya.

A farkon ƙarni na 17 an taɓa kai wata mata mai suna Misis. Phillips" - wadda ake zaton ungozoma ce - a kotu saboda ta yi amani da na'ura wajen gano mai juna biyu.

Wata ma mai suna Catherine Chaire da aka ce ta yi karatun fannin kiyyon lafiya a Landan a wajajen 1590, ta ce "tana iya gane mace mai ciki ta hanyar wanke kayan sawa da sabulu da ruwan da aka rina".

An sha bayar da bayanai barkatai cewa ana amfani da fitsari a bincike da yawa a asibitoci tun a ƙarni na 17.

An taɓa wallafawa a cikin wani littafi mai suna "Cikakken Jagoran Mai Koyo Don Ungozoma" wanda aka wallafa a 1656 cewa, idan aka adana fitsarin mace a cikin wani mazubi mai marufi tsawon 'yan kwanaki to daga baya za a samu "wasu halittu masu rai a ciki"

Amfani da fitsari wajen gudanar da gwaje-gwaje ba baƙon abu ba ne, domin sau da dama yana da alaƙa da abinda muka sani a yanzu.

An bayyana wannan bincike da aka gudanar a shekarar 1930, a matsayin mu'ujizar da bai kamata a yi watsi da ita ba, da kuma ya yi daidai da wani irin sa na farko game da tantance iri kamar yadda aka gano a wani tsarin zamanin zamunna a ƙasar Misira.

Binciken da ya kai ga gano cewa kusan kashi 70 cikin ɗari na lokuta an sha gano cewa fitsarin mace mai juna biyu na samar da maniyi, sai dai hakan bai da wata alaƙar da ka iya samar da cikakken bayanin gano jinsin jinjirin.

Idan aka yi amfani da fitsarin macen da ba ta da juna biyu ba za a ga makamancin haka ba.

Hasalima dai akwai wani sinadari da ake samu a cikin fitsarin mata masu juna biyu, wanda har wani bincike da aka gudanar a ƙarni na 20 ya nuna cewa duk waɗannan gwaje-gwajen da aka gudanar a baya na da wani takamaiman abu da za a iya dogara da shi fiye da wani jiƙo ko maganar wanke kaya da ruwan da aka rina ko kuma binciken da ya bayanna yanayin da mama su ke kasancewa.

An soma amfani da wata hanyar tantance idan mace na da juna biyu a wajajen shekarun 1920 da 1930 ita ce yi wa gafiya ko zomaye wata allura da fitarin mace mai ciki sai a kashe su, bayan an feɗe ne sai a duba a ga idan ƙwayayen haihuwarsu sun canza.

Wannan kenan. Daga baya kuma aka koma amfani da kwaɗi masu rai.

A nan kuma akan duba don gane idan macen da aka yi amfani da fitsarinta wajen yi ma kwaɗon allurar tana da juna biyu, to ita ma macen kwaɗon za ta nasa ƙwai.

An ci gaba da gudanar da irin wannan bincike har wajajen shekarar 1950. Amma fa dukan waɗannan hanyoyin na da matuƙar tsada kuma ba za a iya ci gaba da amfani da su a matsayin cikakkiyar madogara ba, kuma ba su cika dacewa a jikin ɓeraye da kwaɗi ba.

A wajajen 1960 kuma, an samu nasarar fito da irin hanyar da muke amfani da ita a yanzu. sha'anin juna biyu na taka muhimmiar rawa ga tarihin maa a duniya. na Sanin samun ciki babban abu ne da ya zama tamkar gado, daga uwa zuwa uwa.

Wannan tarihin kuwa ya bayyana abubuwan ban mamaki da mutane suka daɗe suna amfani da su wajen gudanar da awon ciki shekaru aru-aru kuwa, tun ma kafin a kai ga tabbatar da sahihincin sakamakon irin binciken da suka gudanar a wancan lokaci.