You are here: HomeAfricaBBC2023 05 25Article 1773884

BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023

Source: BBC

Yadda aka sako ragowar ƴan matan sakandiren Yawuri da aka sace

Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro musamman a arewacin kasan Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro musamman a arewacin kasan

Ƙungiyar iyayen daliban makarantar yan mata ta Yawuri da ke jihar Kebbi ta tabbatar da dawowar daliban makarantar biyu da suka rage a hannun ‘yan bindiga.

Ƴan matan na daga cikin dalibai 11 na kwalejin gwamnatin taryya da ake zargin Dogo Giɗe ya yi garkuwa da su, kuma ya sako su ranar Laraba.

Salim Ka'oje, shugaban ƙungiyar iyayen daliban Makarantar Yawuri da aka sace yaransa ne ya tabbatar da isowarsu gida yau Alhamis. Sannan ya ce cikin daliban da aka ceto har da wata daliba da yan bindigar suka yi dauko daga Kaduna.

Ya bayyana wa BBC cewa zuwa yanzu babu wata ɗaliba da ta rage a hannun ƴan bindigar.

Ka'oje ya ƙara da cewa "akwai wata yarinya da aka kamo daga Kaduna aka haɗa da yaran amma ba ta cikin yaran ƴan makaranta na Yawuri, sai ɓangaren iyaye suka sanya ta cikin tattaunawarsu kuma sun ci nasara, yanzu haka kowa ya dawo gida."

Ya ce tattaunawar da suka yi da ƴan bindigar ba wai ta shafi kuɗin fansa bane, "akwai abubuwa da dama da muka yi tsakaninmu da waɗannan mutane wanda ba zan yi gaggawar faɗinsu ba, sai mun zauna da gwamnati da jami'an tsaro, idan muka tattauna su idan muka ga babu damuwar a faɗa muku, za mu bayyana muku."

Shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban ya kuma ce suna cikin jimami saboda rashin ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar - sakataren kwamitin iyaye 11.

A cewarsa, yaran biyu da suka samu haɗuwa da iyalinsu suna cikin damuwa sai dai duka yaran su uku har da wadda aka karɓo daga Kaduna suna hannun gwamnatin jihar ta Kebbi ana kuma kula da lafiyarsu.

A cikin watan Aprilu ne aka sako ɗaliban makarantar huɗu da suka rage a hannu ƙasurgumin ɗan fashin daji, Dogo Giɗe.

Shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban a lokacin ya ce 'yan matan huɗu sun kuɓuta ne sanadin wani ƙoƙari daga mahaifan ɗaliban da kuma masu tallafa musu.