You are here: HomeAfricaBBC2023 08 27Article 1832843

BBC Hausa of Sunday, 27 August 2023

Source: BBC

Ya kamata a samar da tallafin gwamnati na din-din-din - Masana

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

A Najeriya, yayin da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi ke kokarin samar da tallafin abinci ga al'ummar kasar bayan cire tallafin man fetur, masu sharhi na ganin matakin na wucin-gadi ya dace amma matakin din-din-din zai fi dorewa.

Barista Bello Galadi, tsohon shugaban reshen kungiyar lauyoyi ta Najeriya (wato NBA) a jihar Zamfara, ya shaida wa BBC cewar tunanin bayar da tallafin abin a yabawa gwamnatin tarayya ne idan aka yi la`akari da halin da talaka ya shiga na yunwa da fargaba da tashin hankali.

Barista Bello Galadi ya ce ''Na fahimci wannan mataki ne na wucin gadi, shi ko al`amari irin wannan ya kamata ya zamo mataki ne na din-din-din''.

Ya ce, ''Matsalolin da suka jefa talaka cikin wannan yanayi, sun hada da rashin tsaro wanda ya haifar da tabarbarewar harkokin noma, akwai kuma rufe iyakokin kasa wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da nufin samar da tsarin wadata kasa da abincin cikin gida tsarin da ya dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen waje''.

Barista Bello ya kara da cewar ''Daga wannan lokacin aka shiga wahala a Najeriya, na yar da cewar tsari ne mai kyau a samar da abinci ingantacce to amma tsarin da aka bi wajen kaddamar da shirin shi ya jefa talaka cikin kunci''

Hanyoyin da za a bi wajen samar da tsarin din-din-din.

Barista Bello Galadi, ya ce, ''Da farko gwamnati ta inganta tsaro don manoma su koma gona su noma abincin da zai wadata sannan su kai kasuwanni don sayarwa. Na biyu a bude iyakokin kasa don a shigo da abinci, idan aka yi haka abinci zai wadaci al`umma''.

Menene kalubalen shigowa da abinci daga kasashen ketare?

Baristan ya ce tabbas shigowa da abinci zai iya haifarwa manoma tarnaki, to amma matakan da gwamnati ta dauka game da hana shigowa da abinci sun yi tsauri, kuma kamata ya yi a ce gwamnatin tarayya ta dauki wasu shekaru don samar da abincin cikin gida amma ba tsarin nan take ba.

Mafita

Masanin ya ce, abin da ya kamata a yi don wannan tallafi ya isa ga talakawa shi ne zai yi kyau gwamnatocin jihohi da aka dorawa alhakin rabon tallafin shinkafa, su tabbatar sun sayo kuma sun bayar da ita ga talaka wanda aka kirkiri wannan tsari don shi.

Sannan a sayo abincin a wadace kuma a kafa shaguna a mazabu don sayar da shinkafar a farashi mai rahusa, idan aka yi haka abinci zai wadata cikin sauki, in ji shi.