You are here: HomeAfricaBBC2023 08 11Article 1823264

BBC Hausa of Friday, 11 August 2023

Source: BBC

Wutar daji ta ƙone wani gari ƙurmus a Amurka

Hoton alama Hoton alama

Hukumomi a Hawaii sun ce wutar dajin da ke ci a tsibirin Mau ta ƙone garin ƙurmus wanda kuma ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin jihar da ke Amurka.

Gwamnan tsibirin ya ce zuwa yanzu wutar ta hallaka mutum 55, ana kuma fargabar cewa alkaluman za su iya ƙaruwa.

Jami'ai sun ce wutar ta ɗaiɗaita dubban mutane, kuma ana fuskantar wahala wajen aikin ceron mutane.

Wutar ta kuma lalata muhimman wurare a Hawaii ɗin, ciki har da wani daɗaɗɗen otel da kuma wata itaciya da aka ruwaito cewa ita ce mafi girma a Amurka.

Hukumomi sun kiyasta cewa ɗaruruwan mutane ne suka ɓata, kuma ana fuskantar wahala a aikin nemo su saboda katsewar wutar lantarki da hanyoyin intanet a faɗin tsibirin.

Ɓarkewar wuta daji a tsibirin dai ba sabon abu bane, amma an bayyana wanda ya faru a baya-bayan a matsayin wanda ya fi muni a tarihin jihar.

Hukumomi dai sun ce ba su da matsaniyar abin da ya haddasa gobarar, sai dai suna alaƙanta shi da sauyin yanayi - inda ake ci gaba da bincike.

Jami'an kashe gobara na can suna ta ƙoƙarin kashe wutar wadda iska da fari ke ƙara rurata, amma sun ce sun shawo kan wani ɓangare na wutar.

Wata mata mai suna Teressa Dixon, mazauniyar Lahaina, ta faɗa wa BBC cewa tana dawowa daga aiki ne lokacin da ta ga an rufe hanyar zuwa gidanta.

Ƴar uwarta ce ke kula mata da jarirnta idan ta tafi wurin aiki, amma saboda rashin wayar tarho na nufin cewa ba ta san halin da suke ciki ba.

"Na hau babur domin komawa na duba ƴan uwana. Ba bu abin da nake gani illa wuta tana ci a gidajenmu lokacin da na isa gida," in ji ta.

Ta faɗa wa BBC cewa hayaki ne ya turnuke sararin samaniyar, inda ta taka duwatsu ta faɗi ƙasa wanda ya sa har ta je ta bugu da wani itace da kuma ya sanya ta ji rauni a kafarta.