You are here: HomeAfricaBBC2023 01 27Article 1703246

BBC Hausa of Friday, 27 January 2023

Source: BBC

Wolves za ta dauko Gomes daga kungiyar Flamengo

Gomes (hagu) Gomes (hagu)

Wolves ta amincewa da yarjejeniyar dauko dan kwallon tsakiya da ke murza leda a Flamengo, Joao Gomes.

Dan shekaru 21, tun a shekara ta 2020 ya soma buga wa babbar tawagar kungiyar.

Kocin Wolves, Julen Lopetegui ya bayyana cewa Gomes zai taka muhimmiyar rawa wajen taimakon kungiyar.

Sai dai kungiyar Lyon ta Faransa ita ma tanason dauko Gomes kuma Flamengo ta nuna ashirye take ta amince da yarjejeniyar.

A mako mai zuwa ne ake sa ran Gomes zai shiga Ingila domin a gwada lafiyarsa kafin ya sanya hannu a kwantaragin.