You are here: HomeAfricaBBC2023 08 09Article 1821818

BBC Hausa of Wednesday, 9 August 2023

Source: BBC

Wolves ta nada Gary O'Neil sabon kociyanta

Garry O'Neil Garry O'Neil

Wolverhampton ta sanar da nada tsohon kociyan Bournemouth, Garry O'Neil, a matsayin wanda zai horar da ita.

Tuni ya amince da kwantiragin kaka uku, ya kuma maye gurbin Julen Lopetegui.

An sanar da raba gari tsakanin kungiyar da Lopetegi a Molineu ranar Talata, kwana uku kafin fara kakar Premier League ta 2023/24.

O'Neil ya ja ragamar Bournemouth zuwa mataki na 15 a teburin Premier League a bara, daga baya ta kore shi ranar 19 ga watan Yuni.

Mai shekara 40, shi ne kociyan Wolves na hudu cikin shekara biyu.

Zai fara aiki ranar Litinin, lokacin da Wolves za ta ziyarci Old Trafford domin karawa da Manchester United a wasan farko na Premier League.

Kociyoyi da dama sun nemi aikin horar da Wolves domin maye gurbin Lopetegui, amma O'Neil aka zaba.

Za a fara wasan farko a kakar Premier League ta bana da wasan Burnley, wadda za ta karbi bakuncin Manchester City.