You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853930

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Wolves ta ci Man City karon farko da aka doke ta a Etihad

Hoto daga gasar Hoto daga gasar

Wolverhampton ta kawo karshen wasa shida a jere da Manchester City ta ci a Premier League a bana.

City ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Wolverhapton a wasan mako na bakwai ranar Asabar a Molineux.

Wolves ta fara cin kwallo ta hannun Ruben Dias, minti 13 da fara tamaula, bayan da dan wasan City ta ci gida.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta farke ta hannun Julian Alvarez, amma Wolves ta kara na biyu ta hannun Hee-Chan Hwang.

Pep Guardiola, ya kalli karawar a cikin 'yan kallo, bayan da ya yi hutun kuncin dakatarwa wasa ɗaya da aka yi masa.

City ta yi fatan cin wasa na bakwai a jere da fara Premier League a jere amma hakan bai samu ba, inda kungiyoyi biyu ne ke rike da wannan bajintar.

Chelsea ce mai rike da wannan kambun a kakar 2005/06 da kuma Liverpool wadda ta yi hakan a 2019/20 kuma kowacce sai da lashe Premier League a kakar.

Wolves ta kawo karshen rashin nasara a wasa hudu a dukkan fafatawa, wadda aka doke karo uku da canjaras daya.