You are here: HomeAfricaBBC2023 07 24Article 1811141

BBC Hausa of Monday, 24 July 2023

Source: BBC

Wilfred Zaha ya koma Galatasaray daga Crystal Palace

Wilfried Zaha Wilfried Zaha

Wilfried Zaha ya koma Galatasaray, bayan ƙarewar kwantiraginsa da Crystal Palace a ƙarshen kakar 2022/23.

Zaha, mai shekara 30, ya sa hannu kan yarjejeniyar kaka uku a kan kuɗi fam miliyan biyu inda zai riƙa karɓar albashin fam miliyan 3.75 duk shekara.

Zaha ya fara taka leda a Palace yana da shekara 12, ƙungiyar da ya fi takawa leda tsawon rayuwarsa a sana'ar tamaula.

Ya buga mata wasa 458 kuma shi ne na uku a tarihin yawan ci wa ƙungiyar kwallaye, inda ya jefa mata ƙwallo 90 a raga.

Ya ci wa ƙungiyar ƙwallo bakwai a kakar da ta wuce, ya kuma ɗaura mata ƙyallen kyaftin a karo da yawa.

Zaha ya fara buga wa babbar kungiyar Palace wasa a 2010 yana da shekara 17, daga nan ya zama ƙashin bayan kulob ɗin, har ya taimaka mata wajen komawa Gasar Premier League a 2013.