You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829126

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

West Ham ta doke Chelsea duk da dumbin kudin da ta kashe a bana

Hoto daga gasar Hoto daga gasar

Chelsea ta yi rashin nasara da ci 3-1 a wasan mako na biyu a gasar Premier League da suka fafata a gidan West Ham.

West Ham ce ta fara cin kwalo ta hannun Nayef Aguerd a minti na bakwai da take leda, daga baya Chelsea ta farke ta hannun Carney Chukwuemeka tun kan hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne West Ham mai masaukin baki ta kara na biyu ta hannun Michail Antonio.

Chelsea wadda ta yi ta 12 a kakar da ta wuce, wadda ba za ta buga gasar Zakarun Turai ba a bana ta barar da fenariti ta hannun Enzo Fernandez.

Daf da za a tashi daga karawar West Ham ta samu fenariti, bayan da sabon dan kwallon da tadauka mafi tsada a Birtaniya, Moise Caceido ya yi keta.

Lucas Paqueta dan kwallon tawagar Brazil shi ne ya yi bugun daga kai sai mai tsaron ragar ya kuma zura ta raga.

A bara a irin wannan lokacin a gasar West Ham da Chelsea sun tashi 1-1 ne, yayin da Chelsea ta yi nasara da cin 2-1 a Stamford Bridge.

West Ham mai maki hudu ta tashi 1-1 a gidan Bournemouth a wasan farko ranar Asabar da ta gabata.

Ita kuwa Chelsea maki daya ne da ita bayan da ta yi 1-1 da Liverpool a Stamford Bridge a karawar farko.

West Ham ta karasa fafatawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Nayef Aguerd jan kati, wanda ya ci kwallon farko.