You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811900

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Watford: Sarr ya koma Marseille, Udinese ta dauki Kabasele

Ismaila Sarr (dama) Ismaila Sarr (dama)

Dan wasan gaba na Watford Ismaila Sarr ya koma Marseille ta Faransa, yayin da Christian Kabasele ya koma Udinese kan kudin da ba a bayyana ba.

Sarr, mai shekara 25, ya zura kwallo 34 a raga a wasanni 131 da ya buga wa Watford, bayan da ya koma buga Premier League daga Rennes cikin Agustan 2019.

Ya koma Watford ne kan fan miliyan 27, kawo yanzu Sarr ya zura kwallo 10 a wasa 39 da ya buga a bara a Championship.

Shi kuwa Kabasele, mai shekaru 32, ya buga wasa 25 a kungiyar.

Kabasele ya shafe shekaru bakwai a kungiyar da ke Vicarage Road, bayan da ta dauko shi daga KRC Genk ta Belgium a 2016.

A sakon bankwana da ya aike wa magoya bayansa, ya ce: "Na zo nan ne a matsayin matashin dan wasa, yanzu na tafi a matsayin kwararren dan kwallo.''