You are here: HomeAfricaBBC2023 10 25Article 1868987

BBC Hausa of Wednesday, 25 October 2023

Source: BBC

Watakila a kwashe wa Everton maki 12

Kocin Everton Sean Dyche Kocin Everton Sean Dyche

Everton na fuskantar hukuncin kwashe mata maki 12, idan an kammala binceken da ake mata kan karya dokar hada-hadar kuɗi a Premier League, in ji wani rahoto da aka aka fitar ranar Laraba.

Jaridar 'Daily Telegraph' ta ce mahukuntan Premier League sun buƙaci kwamitin da yake zaman kansa da ya zartar da hukuncin, wanda zai zama na farko da aka kwashe maki da yawa a ƙungiya a tarihin gasar.

Da zarar an cire maki 12 a Everton a wannan lokacin za ta koma ta ƙarshen teburi da rarar maki biyar da za a bi ta.

Kungiyar da Sean Dyche ke jan ragama tana ta 16 a kan teburin mai maki shida, bayan da aka doke ta daga karawa shida a wasa tara da fara kakar nan.

Cikin watan Maris Premier League ta miƙa batun wajen kwamitin bincike kan zargin da ake mata kan karya dokar tsayawa da kafa wajen amfana da samun riba daga ƙarshen kakar 2021-22.

An bai wa ƙungiyar damar rabuwa da kimanin fam miliyan 105 cikin shekara uku, ko kuma ta fuskanci hukunci.

Everton ta yi shekara biyar a jere tana hasarar kasuwanci da ya kai sama da fam miliyan 430 jimilla.

777Partners ne ke ƙoƙarin sayen ƙungiyar, wani kamfani ne daga Amurka na masu zuba hannun jari.