You are here: HomeAfricaBBC2023 02 14Article 1714367

BBC Hausa of Tuesday, 14 February 2023

Source: BBC

Watakila Southampton ta bai wa Marsch aikin horar da ita

Jesse Marsch Jesse Marsch

Southampton na sha'awar bai wa Jesse Marsch aikin kociyanta, domin maye gurbin Nathan Jones.

Kwana takwas da Leeds United ta kori Marsch, wanda yake tattaunawa da kungiyar St Mary, domin cimma matsaya a yanzu haka.

Ranar Lahadi Southampton ta sallami Jones daga aiki, bayan da Wolves ta doke ta 1-0 da hakan ya sa ta zama a karshen teburin Premier.

Kungiyar St Mary za ta ziyarci Chelsea ranar Asabar a gasar Premier, sannan ta kara da Leeds a makon gaba.

Southampton ta hangi masu horar da tamaula da yawa ciki har da Frank Lampard da Wayne Rooney, sai dai salon kocin Marsch ke burge ta.

Kungiyar ta hada maki 15 daga wasa 22 da ta buga a Premier League a bana da cin karawa hudu da canjaras uku aka doke ta 15.

Marsch ake ganin watakila Southampton za ta bai wa aikin, wanda yake da kwarewar da take bukata a Premier League.