You are here: HomeAfricaBBC2023 09 26Article 1851632

BBC Hausa of Tuesday, 26 September 2023

Source: BBC

Watakila Real ta koma ta daya a La Liga idan ta ci Las Palmers

Yan wasan Real Madrid Yan wasan Real Madrid

Real Madrid za ta karbi bakuncin UD Las Palmas ranar Laraba a wasan mako na bakwai a La Liga da za su kara a Santiago Bernabeu.

Real Madrid mai maki 15 ta ci wasa biyar a jere da fara kakar bana, wadda Atletico Madrid ta doke ta a karawar mako na shida.

Las Palmers tana ta 16 a kasan teburi mai maki biyar, wadda ta ci wasa daya da canjaras biyu aka doke fafatawa biyu.

Kawo yanzu Jede Bellingham na Real Madrid ya ci kwallo biyar a wasannin da ya buga wa kungiyar a kakar nan.

Real Madrid wadda take ta uku da maki 15 bayan wasa shida za ta iya koma wa ta daya a teburin La Liga da maki 18.

Barcelona, wadda take jan ragama da maki 17 ta tashi 2-2 da Mallorca ranar Talata a gasar ta La Liga.

Kakar karshe da suka fuskanci juna a La Liga ita ce a 2017/2018

Asabar 31 ga watan Maris din 2018


  • Las Palmas 0 - 3 Real Madrid

Lahadi 5 ga watan Nuwambar 2017


  • Real Madrid 3 - 0 Las Palmas

Sauran wasannin mako na bakwai da za a buga ranar Laraba:


  • Athletic Bilbao da Getafe
  • Villarreal da Girona
  • Valencia da Real Sociedad
  • Cadiz da Rayo Vallecano

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Fran.

Masu tsaron baya: Carvajal, Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger da Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da Ceballos.

Masu cin kwallo: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.