You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824833

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Watakila Mbappe ya ci gaba da zama a PSG

Kylian Mbappe Kylian Mbappe

Kylian Mbappe ya koma yin atisaye, watakila ya ci gaba da zama a Paris St-Germain, mai rike da kofin Ligue 1 na bara.

Dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 24, ya daina atisaye da kungiyar, yayin da PSG ba ta saka shi a wasan lik da ta tashi 0-0 ranar Asabar ba.

Haka kawai dan wasan ya ce ba zai tsawaita zamansa a PSG ba, wanda yake fatan komawa Real Madrid a matakin mara kungiya.

Kyaftin din tawagar Faransa ya kalli karawar a cikin 'yan kallo tare da Ousmane Dembele, wanda ya koma PSG daga Barcelona kan fam miliyan 43.

Haka kuma Mbappe bai buga wa PSG wasannin atisayen da ta buga a Asia ba, don tunkarar kakar tamaula ta bana.

Sauran yarjejeniyar kaka daya ta rage wa Mbappe a PSG, wanda bai amince ya tsawaitata ba.

A watan jiya PSG ta bai wa Mbappe damar ganawa da Al Hilal ta Saudi Arabia, wadda ta yi tayin sayensa kan fam miliyan 259 a matakin mafi tsada a duniya.

Shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi ya dage ba zai bar Mbappe ya bar kungiyar haka ba, zai yi kokari ya sa dan kwallon ya kara saka hannun ci gaba da wasa koda kaka daya daya.

Hakan zai sa dan kwallon ya ci gaba da wasa zuwa karshen kakar 2025, hakan zai ba su damar sayar da shi ga Real Madrid kenan, su samu kudin da suke bukata.

Mbappe, wanda ya koma PSG a 2017 ya fara buga wasannin aro daga Monaco daga baya ta saye shi fam miliyan 165.7, wanda kawo yanzu ya ci kwallo 212 a wasa 260.