You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853939

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Wataƙila Smith Rowe ya bar Arsenal, Ƙungiyoyi na rububin Toney

Emile Smith Rowe Emile Smith Rowe

Ɗan wasan tsakiya a Arsenal da Ingila Emile Smith Rowe, mai shekara 23, na duba yiwuwar barin Emirates idan ba a sa shi a wasa sosai kafin watan Janairu. (90min)

Ƙungiyoyin Wolves da West Ham da Everton da AC Milan na zawarcin ɗan wasan Paris St-Germain Hugo Ekitike, mai shekara 21. (L'Equipe daga Le10Sport )

Newcastle ta bi sahun Arsenal da Tottenham da Manchester United da Chelsea a neman Ivan Toney, duk da cewa zai yi wahala Brentford ta amince ɗan wasan mai shekara 27 ya tafi a watan Janairu. (The i )

Manchester City ta bi sahun Chelsea a farautar ɗan wasan baya a Italiya da Inter Milan Federico Dimarco, mai shekara 25. (Calciomercato)

Chelsea na da sauran fata kan ɗan wasan Netherlands Ian Maatsen, mai shekera 21, zai sanya hannu a sabon kwantiraginsa. A karshen wannan kaka kwantiragin da yake kai a yanzu ke karewa. (Football Insider)

Brighton na sha'awar ɗan wasan Sifaniya Nico Williams, mai shekara 21 daga Athletic Bilbao. (Fichajes - in Spanish)

Ƙungiyoyi da dama irin su Manchester United da Liverpool da Brighton da West Ham da Barcelona da Ajax na bibbiyar cigaban ɗan wasan Royal Antwerp mai shekara 18 daga Belgium Arthur Vermeeren. (Mundo Deportivo)

Manchester United na burin cimma yarjejeniya da ɗan wasan Nice na Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 23, da kuma ɗan wasan Burkina Faso da Bayer Leverkusen Edmond Tapsoba, mai shekara 24. (Fabrizio Romano)

Mai Paris St-Germain Nasser Al-Khelaifi ya dage cewa makomar ɗan wasansu Kylian Mbappe mai shekara 24 za ta ci gaba da kasancewa da kungiyar ta Lig 1. (FourFourTwo)

Kocin Roma Jose Mourinho na son ya sake ɗauko ɗan wasan Tottenham da Ingila Eric Dier mai shekara 29. (Mirror)

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Manchester United da kuma ke wasa a Ingila Jesse Lingard ya sa West Ham ta tafka asarar kuɗaɗe, yanzu haka dai yana atisaye da ƙungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya. (Mirror)

Barcelona na gab da sabonta yarjejeniyar Frenkie de Jong, mai shekara 26, yayin da Manchester United ke ci gaba da nemansa. (Fichajes)

Rahotanni na cewa ɗan wasan baya na Jamus Jerome Boateng ya kira shugaban Real Madrid Florentino Perez inda yake neman aiki bayan ƙarewar kwantiraginsa a Lyon, yanzu dai ɗan wasan mai shekara 35 ba shi da ƙungiya. (Bild)