You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798550

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Wasu na ƙorafi, NNPP na dariya a kan shugabancin Majalisar Najeriya

Jagoran NNPP Rabiu Musah Kwankwasa da alamar kungiyar Jagoran NNPP Rabiu Musah Kwankwasa da alamar kungiyar

Ra'ayoyi sun sha bamban musamman tsakanin jam'iyyun siyasar Najeriya bayan fitar da sabbin manyan jami'an Majalisar Tarayya ta goma.

Awanni bayan sanar da jagororin, manyan jam'iyyun APC da PDP da suka mamaye zaurukan majalisun guda biyu, sun nuna rashin jin daɗi da sunayen da aka fitar a Majalisar Dattijai da ta Wakilai.

Jam'iyyar APC mai mulki ce ta mamaye kujeru guda takwas na ɓangaren masu rinjaye a majalisun biyu, ƙarƙashin jagorancin Sanata Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai.

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta tashi da kujera huɗu: shugaban marasa rinjaye a duka majalisun guda biyu da mataimakin shugaban marasa rinjaye a majaisar dattijai, sai kuma kujerar mai tsawatarwa na majalisar wakilai.

LP da NNPP kuma sun raba kujeru guda huɗu na ɓangaren marasa rinjaye, a majalisar dattijai, LP ta samu kujerar mai tsawatarwa, sai mataimakin mai tsawatarwa a majalisar wakilai. Inda NNPP take da kujerar mai tsawatarwa, amma a majalisar dattijai sun samu mataimakin mai tsawatarwa.

Sai dai, ba ƙuri'a aka kaɗa kafin fitar da sabbin shugabannin ba a ranar Talata, majalisun tarayyar dai sun ce matsaya ce 'yan majalisun daga rukunonin jam'iyyunsu kawai suka cimma.

Wannan dai wani sabon al'amari ne ga ƙananan jam'iyyun adawa a Najeriya. Wani jigo a jam'iyyar NNPP ya faɗa wa BBC cewa abin da suka samu a shugabancin majalisun biyu "wanda zai je sama ne ya taka leda".

Mallam Buba Galadima ya ce ba su ma sa rai, 'ya'yan jam'iyyarsu za su samu wannan tagomashi a Majalisar Tarayya ta goma ba. Jam'iyyar LP wadda ta garzaya kotu don ƙalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu da APC, mai yiwuwa wannan kaɓaki zai sa wasu 'ya'yanta a majalisun tarayyar su fara canza tunani.

Sai dai yayin da a iya cewa wasu na murna har kunne, ga alama jam'iyyun APC da PDP ba su karɓi kason cikin daɗin rai ba.

Rahotanni sun ambato shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu na cewa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar bai amince da 'yan majalisar da aka bai wa muƙaman masu rinjayen ba.

'Jita-jita' da kuma ɓaraka a APC

Da yammacin Talata ne, shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya gana da gwamnoni da kuma magoya bayan jam'iyyar a Abuja, jim kaɗan bayan sanar da sunayen shugabannin.

A wurin taron ne kuma aka ambato shi ya na bayyana cewa ba da amincewarsu aka sanar da sunayen waɗannan 'yan majalisa ba, ya bayyana sanarwar a matsayin wata "ji-ta-ji-ta a intanet".

"Shugabancin jam'iyyar [APC] da kwamatin gudanarwarta ba su taɓa faɗa wa wani, mutanen da suka zaɓa a shugabancin majalisar ba," in ji shi.

"Kuma sai mun daddale, sannan za mu aika da matsayarmu a rubuce, wanda shi ne al'ada...ban da haka, duk wata sanarwa da aka bayar, ba daga wajenmu take ba."

Sai dai, jim kaɗan bayan kammala taron ne kuma Gwamnan jihar Ebonyi Hope Uzodinma, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma ya halarci taron na yammacin Talata, ya ce da goyon bayan jam'iyyar aka yi zaɓin.

"Shugabannin majalisar 'yan jam'iyyarmu ne kuma muna goyon bayansu. Idan akwai wata ɓaraka za mu nemo hanyar magance ta a cikin gida, amma dai ƙungiyar gwamnoni na goyon bayansu, jam'iyya ma tana tare da su," a cewarsa.

Ita dai APC ga alama tana ƙorafi ne a kan mutanen da aka bai wa muƙaman, ba wai adadin abin da ta samu ta raina ba.

An yi mamaki da irin wannan martani daga jam'iyyar mai mulki ganin yadda ta yi uwa, ta yi makarɓiya wajen tabbatar da zaɓen Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattijai, da Tajuddeen Abbas, a muƙamin shugaban majalisar wakilai cikin tsakiyar watan jiya.

Sai dai wani ɓangare da ba a ji martaninsa ba a kan sabbin shugabannin majalisun, shi ne masu zartarwa. Kamar jam'iyyarsu ta APC, da tabarrakin ɓangaren zartarwar ne Akpabio da Abbas suka ci zaɓen shugabancin da suke kai yanzu.

_____________________________________________________________________________

Jagororin Majalisar Dattijai:

  • Sanata Opeyemi Bamidele - Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ekiti (kudu maso yamma)


  • Sanata David Umahi - Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ebonyi (kudu maso gabas)


  • Sanata Ali Ndume - Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Borno (arewa maso gabas)


  • Sanata Lola Ashiru - Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Kwara (arewa ta tsakiya)


  • Sanata Simon Davou na PDP - Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Filato (arewa ta tsakiya)


  • Sanata Oyewunmi Olarere na PDP - Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Osun (kudu maso yamma)


  • Sanata Darlington Nwokeocha na LP - Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Abiya (kudu maso gabas)


  • Sanata Rufai Sani Hanga na NNPP - Mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Kano (arewa maso yamma)


  • Jagororin Majalisar Wakilai:

  • Julius Ihonvbere: Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Edo (kudu maso kudu)


  • Halims Abdullahi: Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Kogi (arewa ta tsakiya)


  • Bello Kumo: Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Gombe (arewa maso gabas)


  • Adewunmi Onanuga: Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Ogun (kudu maso yamma)


  • Kingsley Chinda: Shugaban Marasa Rinjaye (PDP) daga Jihar Ribas a (kudu maso kudu)


  • Aliyu Madaki: Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye (NNPP) daga Jihar Kano a arewa maso yamma


  • Ali Isah: Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye (PDP) daga Jihar Gombe a arewa maso gabas


  • George Ozodinobi: Mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye (LP) daga Jihar Anambra a kudu maso gabas

  • _____________________________________________________________________________

    Rigimar ƙarfin iko a PDP

    Duk da yake, ita ce ke da kujeru mafi yawa a majalisun kuma ta samu dukkan kujerun shugabancin marasa rinjaye, PDP dai ba ta gamsu ba.

    Tun farko jam'iyyar ta nemi Shugaban Majalisar Dattijai, Akpabio ya jinkirta sanar da sunayen, ta ce ba ta kammala cimma matsaya game da zaɓen shugabannin ba tukunna.

    Cikin 'yan PDP da suka nemi shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai akwai Sanata Aminu Waziri Tambuwal da kuma Sanata Adamu Aliero, dukkansu babu wanda ya yi nasarar samun kowannen irin muƙami a ranar Talata.

    Akwai raɗe-raɗin cewa, 'yan majalisar da suka yi nasarar zama jagororin suna da alaƙa da Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas, mai adawa da shugabancin jam'iyyarsu ta PDP.

    Wike ya fara adawa da Tambuwal da kuma shugabannin PDP tun cikin watan Mayun 2022, bayan kammala zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa, inda Tambuwal ɗin ya haɗa kai da Atiku Abubakar wajen kayar da Wike.

    Ana kuma ganin Nyesom Wike yana ci gaba da aiki da Bola Ahmed Tinubu, har ma an yi imani cewa ya ba shi gudunmawa wajen samun nasarar cin zaɓen shugaban ƙasa.

    Amma sabon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Simon Davou ya kare tsarin da aka bi wajen zaɓensu.

    "Abokan aikinmu 50 ne suka amince. A madadin a zauna a ofishin jam'iyya a yanke shawara, abin ya fi kama da cewa 'yan majalisar da aka zaɓa daga jam'iyyu guda shida ne suka yanke hukuncin," a cewarsa.

    Ya yi iƙirarin cewa 'yan majalisa 38 cikin 50 a ɓangaren marasa rinjaye ne suka amince kafin a sanar da sunansa.

    Sai dai PDP ta faɗa wa BBC cewa babu wani mataki da za ta ɗauka a kan abin da ya faru "saboda ba abu ne da ya saɓa wa tsarin mulki ba".

    "Babu wani mataki da za mu iya ɗauka sai dai mu je kotu, idan muka je kotu kuma sai dai mu kawo dokar da aka karya [wadda babu ita]," in ji wani mai magana da yawun PDP, Ibrahim Abdullahi.

    NNPP ce ta fi caɓawa

    NNPP ce ta tashi da kujera biyu a ɓangaren marasa rinjaye, inda Sanata Rufai Sani Hanga ya samu mataimakin mai tsawatarwa a Majalisar Dattijai, shi kuma Ali Madaki ya zama mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai.

    Ta samu kujerun ne duk da yake, ita ce ta uku a yawan kujeru a ɓangaren jam'iyyun adawa.

    Mallam Buba Galadima ya ce sakamakon fitar da sunayen shugabannin majalisar ya zo musu da mamaki. "Gaskiya, abu ne da ba mu sa rai da shi ba."

    Ya ce tun da aka fara gwagwarmayar neman kujerun shugabancin majalisun guda biyu, jam'iyyar NNPP ta bai wa 'yan majalisarta damar su yi aiki da duk wani ɓangare da zai zo musu da buƙatar neman goyon baya da yin tafiya tare.

    Buba Galadima ya ce sun fahimci cewa sha'anin tafiyar da majalisar tarayya abu ne mai matuƙar sarƙaƙiya kuma a wasu lokuta 'yan maalisar ba sa la'akari da bambancin jam'iyya wajen gudanar da wasu harkoki.

    Wasu masana harkokin siyasa kamar Farfesa Kamilu Sani Fagge na ganin cewa dabarar da NNPP ta yi amfani da ita, ta biya mata buƙata don kuwa ta fi caɓawa a cikin harkar.

    "Abin ya fi yi wa NNPP kyau ganin yadda ta samu kujera biyu a cikin takwas, duk da yake, ba ita ce ta biyu a ɓangaren marasa rinjaye ba" a cewar malamin na Jami'ar Bayero ta Kano.

    Jam'iyyar SDP da ke da sanatoci biyu ba ta samu komai ba

    Bugu da ƙari, 'yan majalisar biyu duka 'yan Kano ne. Sai dai Farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Jihar Kaduna na ganin hakan ba zai yi wani tasiri ba, sai dai fa idan sun sanya buƙatun jama'ar da suke wakilta a gaba.

    'Ya kamata PDP ta samu kujeru fiye da haka'

    Duk da yake, PDP ce ke da muƙami huɗu cikin takwas, Farfesa Kamilu Fagge na da ra'ayin cewa kamata ya yi a ce ta samu fiye da haka.

    Jam'iyyar ce ke da muƙamin shugaban marasa rinjaye a majalisun, da kuma mataimakin shugaban a Majalisar Dattijai, da mai tsawatarwa na Majalisar Wakilai.

    PDP na da kujera 36 cikin 109 na sanatoci idan aka kwatanta da takwas na jam'iyyar LP da kuma biyu na NNPP. Sannan babbar jam'iyyar adawar tana da 'yan majalisar wakilai aƙalla 118 cikin 360.

    "Da tsari aka bi na jefa ƙuri'a, da PDP ce za ta kwashe komai a ɓangaren marasa rinjaye domin ta fi sauran yawa," a cewarsa.

    Farfesa Abdulkadir yana ganin PDP na ƙorafi game da zaɓen ne saboda Sanata Aminu Tambuwal, wanda ta mara wa baya, bai yi nasara ba.

    Da yake zantawa da BBC, sabon mai tsawatarwa na majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume ya ce majalisa ta yi la'akari ne da abubuwa da dama wajen cimma matsaya a kan sabbin shugabannin.

    Ya kuma yi watsi da tunanin cewa shugabancin majalisar na iya zama ɗan amshin shata ga ɓangaren zartarwa. A cewarsa, tsarin da majalisar ta bi wajen fitar da shugabannin bai saɓa da abin da aka saba gani a baya ba.