You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280497

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

Wasika daga Afirka: Yadda gawar Mugabe ke ci gaba da haifar da ruɗani a Zimbabwe

Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe

A jerin wasiƙunmu na Afrika, ɗan jarida kuma lauya ɗan asalin Zimbabwe Brian Hungwe ya yi nazari kan yadda shugaban da ya fi daɗewa kan mulki Robert Mugabe, wanda ya mutu a 2019 yake ci gaba da yin tasiri a ƙasar daga cikin ƙabarinsa.

Iyalan Robert Mugabe sun ce ya mutu cikin ɗacin rai kusan shekaru biyu bayan an tilasta masa miƙa mulki ga shugaba na yanzu Emmerson Mnangagwa - kuma ɓacin ransa, har zuwa mutuwarsa na ci gaba da haifar da ruɗani.

Bisa wata al'adar mutanen Afrika, matacce na iya magana, yawanci ta hanyar fitowa a fatalwa da wasu kan yi imanin matacce na iya sake bayyana domin rama zaluncin da aka yi masa.

Idan za a iya auna halin Mugabe a rayuwa ta zahiri dangane da tsananin tunanin da yake da shi na martani, zai iya kasancewa kamar amon narkakken dutse da ke warwatsuwa - irin dutsen Nyiragongo a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da ke luƙume duk abin da ya ci karo da shi.

Mugabe mabiyin ɗarikar Katolika ne, wanda ya samu tarbiya daga ƴan mishan da suka yi tasiri a rayuwarsa. Amma kuma bai yi watsi da al'adunsa ba.

Gwarzon siyasa 'mai ƙarfin iko'

Sau da dama a wurin da ake binne ƴan mazan jiya, Mugabe kan yi kwatance da tasirin ƴar gwagwarmayar ƴanci, Mbuya Nehanda, wadda turawan mulkin mallaka suka rataye a ƙarshen ƙarni na 19.

An yi imani da abin da ta bayyana cewa kasusuwanta za su yaƙi turawan mulkin mallaka. Wani abin da aka yi imani da shi da ya yi tasiri ga ƴan gwagwarmaya masu kishin ƙasa.

A makon da ya gabata shugaba Mnangagwa ya ƙaddamar da mutum mutumin Nehand a tsakiyar Harare, babban birnin Zimbabwe.

Wasu na ganin hakan a matsayin wata dabara ce ta mayar da hankali ga nasarorinta, ganin cewa shirinsa na binne wanda ya gada mai shekara 95 a wurin da ake binne muhimman mutane a ƙasar ya gagara.

Wannan zai ba shi damar kai ziyara hubbaren, tare da samun tabarrakin Mugabe a burinsa na siyasa - duk da cewa shi ya kawar da tsohon abokinsa daga mulki a shekarar 2017, wanda hakan ya hana burin matar Mugabe Grace Mugabe na zama shugabar ƙasa cika.

Misis Mugabe ta hana wa Mista Mnangagwa samun damar, inda ta nace cewa, tsohon shugaban ne ya bar wasiya ga iyalinsa a binne shi a cibiyarsa Zvimba, kusa da mahaifiyarsa Bona.

Masanin halayyar dan adam Joost Fontein - marubucin littafin siyasar matattu a Zimbabwe: Kasusuwa, Jita-jita da fatalwa- ya ba da wani bayani na daban game da matsayar matar tsohon shugaban.

"Ba ta son a binne shi kusa da Sally (Matar Mugabe ta farko) saboda ta san cewa Sally ta fi ta yin fice fiye da yadda take tunani.

"Amma kuma wataƙila tana neman hana wa sabuwar gwamnatin damar alhakin binne Mugabe a inda ake binne manyan ƙasa," in ji shi.

Wannan rikicin ya sake tasowa a watan da ya gabata, inda wani basarake a Zvimba ya zartar da hukuncin kama matar Mugabe da laifin saɓa al'adun gargajiya bayan ta binne mijinta a bayan gidansa.

Misis Mugabe - wasu rahotanni sun ce ba ta da lafiya, tana Singapore - ba ta halarci kotun basaraken ba, amma ya umarci ta biya tara ta shanu biyar da kuma akuya.

Ɗan uwan tsohon shugaban Leo Mugabe ya yi watsi da hukuncin, yana mai cewa sarkin ba shi da ƴancin zartar da hukunci kan batun.

Umarnin miƙa tufafin Mugabe

Duk da haka, rikicin ba abin mamaki ba ne. Farfesa Fontein ya nuna cewa a Zimbabwe muhimmancin mutuwa, ƙasusuwa, da fatalwa na iya shafar siyasa.

"Ce-ce-ku-cen da ya dabaibaye binne Mugabe yana da nasaba da tsarin tunawa da mazan jiya inda shi kansa tsohon shugaban ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatarwa da kuma jajircewa akai sosai," a cewarsa.

A hukuncinsa, basaraken ya buƙaci a sake tono gawar Mugabe a sake binne ta a babbar makabartar ƙasa tare da ba matarsa umarnin ta tattara kayansa da duk abin da ya mallaka ta gabatar da su kafin 1 ga watan Yuli.

Masanin tarihi Terence Ranger ya ce muhimmancin kula da mamaci ya dogara ne da tunanin kariyar da za ba wadanda ke raye.

Ɗan uwan Mugabe Patrick Zhuwao ya ce girmamawar da sarakunan gargajiya suka ba tsohon shugaban ƙasar a matsayin shugaban Zimbabwe za ta iya zama dalilin rikicin.

Wannan ne, kamar yadda ya shaida wa kafar talabijin ta Afirka ta Kudu SABC cewa, abin da Mnangagwa yake so ya samu.

Tsoron maita

Mai magana da yawun shugaba Mnangagwa George Charamba, wanda ya riƙe muƙamin zamanin tsohon shugaba Mugabe, ya musanta tunanin cewa tsohon shugaban yana da wata sandar girma da wanda ya gaje shi yake so.

A yanayi na ruɗanin siyasar gargajiya, ana iya zargin kasusuwa da maita.

An daɗe ana jita-jita cewa Misis Mugabe ta nace ta binne mijinta a gidansa domin daƙile duk wani yunƙuri na tono gawarsa domin amfani da kasusuwansa don cutar da ita da ƴaƴanta.

Akwai masu tunanin cewa tana son ta kasance mai kula da gawar mijinta da kasusuwansa don ƙara wa kanta ƙarfi - ƙarfin da Mugabe ya nuna a tsawon shekaru 37 da ya kwashe yana mulki da kuma wanda ya ba ta ta hanyar "fatalwa."

Ayyukan asiri na siyasa da ake ganin Mugabe ya gina kansa na ci gaba da wanzuwa, inda jagoran kafa Zimbabwe ke ci gaba da haifar da ruɗani daga ƙabarinsa.