You are here: HomeAfricaBBC2023 03 28Article 1739537

BBC Hausa of Tuesday, 28 March 2023

Source: BBC

Wasa 10 ya rage wa Arsenal ko za ta dauki Premier League?

Kocin Arsenal Mikel Arteta Kocin Arsenal Mikel Arteta

Ranar Asabar za a ci gaba da wasannin mako na 29 a gasar Premier League ta kakar 2022/23.

Arsenal ce ta daya a kan teburi mai maki 69 da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City mai maki 61, mai rike da kofin bara.

Kawo yanzu Arsenal wadda ke fatan lashe Premier League na bana a karon farko tana da sauran wasa 10 a gabanta, kafin karkare kakar bana.

Cikin karawa da suka rage mata, za ta yi wasa biyar a Emirates, sannan ta buga sauran biyar a waje.

Cikin wasannin da Gunners za ta yi masu zafi har da wanda za ta kece raini da Manchester City da Liverpool da kuma Chelsea.

Haka kuma Gunners za ta buga wasan hamayya da West Ham a kungiyoyin birnin Landan da na kalubale da Newcastle United.

Tuni Sporting ta fitar da Arsenal a Europa League, sannan Manchester City ta yi waje da ita a FA Cup.

Brighton ce ta fitar da Arsenal a League Cup na bana, yayin da Manchester United ce ta lashe Carabao Cup na kakar nan.

Kenan kofin Premier League ne kadai a gaban Arsenal da take son dauka, domin ta koma buga Champions League a badi.

Rabon da Gunners ta lashe Premier League tun kakar 2003/04 karkashin Arsene Wenger, sai dai tana da shi 13 jimilla.

Manchester United ce kan gaba a yawan daukar babban kofin tamaula a Ingila mai 20, sai Liverpool mai 19.

Wasa 10 da suke gaban Arsenal a Premier League:

Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu

  • Arsenal da Leeds

  • Ranar Lahadi 9 ga watan Afirilu

  • Liverpool da Arsenal

  • Ranar Lahadi 16 ga watan Afirilu

  • West Ham da Arsenal

  • Ranar Juma'a 21 ga watan Afirilu

  • Arsenal da Southampton

  • Ranar Laraba 26 ga watan Afirilu

  • Man City da Arsenal

  • Ranar Asabar 29 ga watan Afirilu

  • Arsenal da Chelsea

  • Ranar Lahadi 7 ga watan Mayu

  • Newcastle da Arsenal

  • Ranar Asabar 13 ga watan Mayu

  • Arsenal da Brighton

  • Ranar Asabar 20 ga watan Mayu

  • Nottingham Forest da Arsenal

  • Ranar Lahadi 28 ga watan Mayu

  • Arsenal da Wolves

  • Wasannin mako na 29 da za a buga a Premier League

    Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu

  • Manchester City da Liverpool


  • Arsenal da Leeds United


  • Crystal Palace da Leicester City


  • Nottingham Forest da Wolverhampton


  • Bournemouth da Fulham


  • Brighton da Brentford


  • Chelsea da Aston Villa


  • Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu

  • West Ham United da Southampton


  • Newcastle United da Manchester United


  • Ranar Lahadi 3 ga watan Afirilu

  • Everton da Tottenham