You are here: HomeAfricaBBC2023 07 28Article 1814177

BBC Hausa of Friday, 28 July 2023

Source: BBC

Wane ne sabon shugaban Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani?

Mohamed Bazoum, shugaba da anka cire a mulki Mohamed Bazoum, shugaba da anka cire a mulki

A yini na biyu bayan sojoji sun bayyana cewa sun tuntsurar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, Janar Abdourahmane Tchiani (wanda ake kira Omar Tchiani) ya bayyana a kafar talabijin inda ya yi wa al'umma jawabi.

Ta tabbata cewa shi ne sabon shugaban ƙasar.

Kafin juyin mulkin shi ne kwamandan rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa.

Juyin mulkin dai ya kawo ƙarshen milkin gwamnatin farar hula da ta karɓi mulki daga farar hula cikin lumana tun bayan komawar ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya a 1960.

Ƙarfin iko

Janar Tchiani ne kwamnadan rundunar tsaron fadar shugaban ƙasar tun daga shekarar 2011.

Mahamadou Issoufou, wanda Bazoum ya gada ne ya kafa rundunar, don samun kariya daga yunƙurin kifar da gwamnatinsa daga dakarun soji, saboda a lokacin an yi juyin mulki har sau hudu a Nijar tun bayan samun yancin kai daga Faransa.

Rundunar tana da dakaru 700, kamar yadda jaridar Jeune Afrique ta bayyana a matsayin ''waɗanda suka samu horo sosai kuma masu ƙarfi.''

Duk da cewa bai bayyana ba a cikin bidiyon da sojoji suka sanar da juyin mulkin, amma an riga an yi yaƙinin cewa Tchaini ne zai jagoranci gwamnatin mulkin sojin.

An kuma alaƙanta Tchiani da yunƙurin kifar da gwamnatin Issoufou a 2015, amma ya bayyana gaban kotu a 2018, inda ya musanta zargin.

Lokuta da dama dai tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci Bazoum ya ci gaba da riko da rundunar tsaron fadar shugaban ƙasar a yadda take, ciki har da Tchiani wanda ya kawar da yunƙurin juyin mulki na 2021.

Sai dai kuma jaridar L'Enqueteur ta ce a ranar 27 ga watan Yuli, kafin juyin mulkin, Bazoum ya so cire Janar ɗin, daga cikin ƙoƙarinsa na aiwatar da sauyi a shugabancin dakarun ƙasar.

A watan Afirilu, Bazoum ya canza babban hafsan sojin ƙasar, lamarin da jaridar Jeune Afrique ta ce ya janyo rashin aminci ga shugaban, a tsakanin dakarun rundunar sojin.

A ranar 27 ga watan Yuli, masu sharhi a gidan talabijin ɗin TV5 Monde sun ce ƙalubalen da suka haɗa da rashawa, da ƙabilanci da kuma rashin kayan aiki a rundunar sojin ne suka tunzura juyin mulkin.

Rayuwarsa a taƙaice

Shekarun Janar Tchiani 62, kuma shi ne kwamandan rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa tun daga shekarar 2011.

A shekarar 2018 tsohon shugaban ƙasar Issoufou ya naɗa shi muƙamin janar.

Babu wani bayani mai yawa a kan tarihin rayuwarsa, da karatu da kuma aikin sojinsa.

Amma kafafen yaɗa labaran Nijar sun riƙa wallafa labari kan shi a bisa zargin hannunsa a yunkurin juyin mulkin 2015 kuma daga bisani kotu ta wanke shi a shekarar 2018.

Bayanai daga wasu kafofi

“Bayan yin juyi mulki tare da tsare shugaba Bazoum, Tchiani ya gaza samun goyon bayan sauran dakarun soji don tabbatuwar juyin mulkin. Da farko babbar rundunar tsaron ƙasar (National Guard) ta nuna rashin goyon bayan yunƙurin, kamar yadda bayanai suka nuna. Yanayin ya ƙara zafi inda ɓangarori suka yi barazanar amfani da ƙarfi kan juna... an riƙa tattaunawa, kafin daga baya aka cimma matsayar da ta kai ga jawabin da sojojin suka karanta.” Radio France Internationale, 27 ga watan Yulin 2023.

"Lokacin da ya miƙa mulki ga Mohamed Bazoum a 2021, Mahamadou Issoufou ya nemi alfarmar a ci gaba da barin jiga-jigan gwamnatinsa cikin sabuwar gwamnatin Bazoum, ciki harda Janar Tchiani. Bazoum ya tsinci kansa cikin tsaka mai wuya, a gefe yana ƙoƙarin tabbatar da gwamnatinsa amma ba ya son yin gaggawar gudanar da sauyi a dakarun sojin." Jeune Afrique, 27 ga watan Julin 2023.

Juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yulin ya ƙara jefa yankin Sahel cikin halin rashin tabbas bayan wani irin sa ya faru a Burkina Faso da Mali masu maƙwabtaka da Nijar.

Bazoum wanda ya fara da tangal-tangal a 2021 biyo bayan yunƙurin juyin muki, yana da kyakkyawar alaƙa da ƙasashen yamma. Ya mayar da Nijar cibiyar shirin wanzar da tsaro ta ƙasashen yankin da ma duniya baki ɗaya, da nufin tabbatar da tsaro a yankin Sahel.

Rikicin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a arewacin Mali cikin 2012 ya ƙara taɓarɓarewa cikin shekarun da suka biyo baya, hakan kuma ya ruruta tashin hankali a Burkina Faso da Nijar.

Matkin da Mali ta ɗauka na rungumar mayaƙan haya na Wagner daga Rasha ya sa Faransa ta janye jikinta daga ƙasar cikin laluma, tare da kawo ƙarshen aikin wanzar da zaman lafiya da dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya akalla 13,000 ke yi a Mali.

Sai dai kuma, Bazoum ya yi maraba da dakarun zuwa birni Yamai, daga cikin dabarunsa na kare Nijar da sauran ƙasashen yammacin Afirka daga rikicin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi irin su IS da kuma al-ƙa'ida

Kifar da gwamnatinsa da Janar Tchiani ya yi a yanzu kuma za ta zamo barazana ga waccan haɗaka.