You are here: HomeAfricaBBC2023 07 06Article 1799339

BBC Hausa of Thursday, 6 July 2023

Source: BBC

Wane ne Messin Turkiyya da Real Madrid ke nema

Messin Iran Messin Iran

Mun ga Messin Iran da Messin Jamus da Messin Scottland da wasu masu yawa.

Amma yanzu lokaci ne da za mu ce barka ga Messin Turkiyya - Arda Guler.

Yaron da ake kwatantawa da gwarzon Argentina Lionel Messi yanzu ya sha kan mafi yawan matasan 'yan wasa, musamman waɗanda suka ƙware wajen yanka da wasa da kwallo, wani abu da ɗan wasan mai shekara 18 ya kware a kai.

Ya zuwa yanzu babu wani ɗan wasa da ya kai inda matashin ya kai, cikin waɗanda suka gabace shi kamar su Sardar Azmoun da Marko Marin da kuma Ryan Gauld. Duka babu wanda ya yi kusa.

Akwai kwarin gwiwar matashin ɗan wasan mai basira Guler zai iya zama ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan da za su yi suna a duniya, a yanzu kuma ƙaddara na neman kai shi gasar da mutumin da ake kwatanta shi da shi ya buga a ƙungiyar da ya yi adawa da ita.

Tun daga lokacin da ya fara buga wa tawagar Fenerbache wasan farko, manyan ƙungiyoyin kwallon ƙafa na Turai suka fara bayyana maitarsu a fili kan ɗan wasan.

Ƙungiyar da Messi ya buga wa ƙwallo Barcelona ta nuna muradinta a fili na ɗaukar ɗan wasan, kuma shugaban ƙungiyar Joan Laporta ya aika daraktan wasannin ƙungiyar Deco domin ya tattauna kan batun.

Abu ne mara daɗi ga ƙungiyar ta Cataloniya ganin yadda ɗan wasan ya zaɓi babbar abokiyar hamayyarta a matsayin wadda yake so maimakon ita, zai koma Madrid a matsayin mafi basira daga yankinsu da ya buga kwallo a Bernabeu.

Wani abu da ya burge masu dillancin ɗan wasan shi ne yadda ƙungiyoyi suka yi ca a kan ɗan wasan - irin su Bayern Munich da Borussia Dortmund da Paris St-Germain da kuma uku daga Premier Ingila Arsenal da Manchester United da Newcastle.

Rahotanni sun bayyana cewa an ta taya shi yuro milyan 17.5, abin da ya sanya ba shi damar ƙara buga wasanni masu yawa a ƙungiyarsa.

Wannan wani ɗan wasa ne da aka amince ya fara yi wa babban kulob ɗinsa wasa a shekaru 16, inda ya shiga a matsayin canji a minti na 66 a wasan da Fenerbache ta yi nasara a HJK Helsinki 1-0 a wasan farko na neman shiga gasar Europa a ranar 19 ga watan Agustan 2021.

Yaron da ya bayar da kwallo aka ci a wasan Super Lig na farko, ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya ci kwallo a wasan 5-2 a ranar 13 ga watan Maris 2022, kwana 16 daga shigar sa shekara ta 17.

Duka dai, yana da kwallo bakwai ya kuma ba da bakwai an ci a minti 1,187 na Super Lig da ya buga, ma'ana ya yi wani abu na cin kwallo a kowanne minti 85 na wasa.

Ba shi lamba 10 da aka yi a Fenerbache na nuni da yadda ya samu shiga cikin ƙungiyar sosai. Rigar da a baya manyan 'yan wasa irin su Tuncay Sanli da Robin van Persie da kuma Mesut Ozil, mafi mahimmanci shi ne Alex gwarzon ƙungiyar ta Istanbul wanda ya ci kwallo 171 ya ba da 136 aka ci a wasa 344 tsakanin 2004 zuwa 2012 kuma aka yi mutum-mutuminsa a wani wuri a garin.

Idan har za a iya kwatanta Guler da wani ɗan wasa shi ne tsohon ɗan Brazil ɗin.

A ƙarshe, ba ya fargabar gwada wani abu, misali shi ne kwallo da ya ci daga wajen yadi na 20 a wasan da suka ci 5 -1 a watan Janairu da Kasimpasa.

Ya yi wasansa na farko a ƙasa a wasan sada zumunta da suka yi da Jamhuriyar Czech a ranar 19 da watan Nuwamba 2022, ya ci kwallonsa ta farko a watan Yunin nan da ya gabata, a wasansa na huɗu.

Abin tambayar a nan shi ne wannan lokacin shi ne mafi dacewa ga ɗan wasan ya tsallaka mataki na gaba a rayuwar kwallonsa?

Tsohon ɗan wasan gaban Fenerbache, Ozil, wanda Guler ya gada, wanda ya tafi Real Madrid yana da shekara 21, ya shawarci matashin da ya ƙara shekara guda a Turkiyya domin ƙara samun gogewa.

Da alama da wannan cinikin da Madrid ke yi tana ƙara neman haɗa wasu sabbin zubi na Galacticos.

Akwai 'yan wasan gaba masu tashe, Vinicius Jr da Rodrygo da suke a ƙungiyar dama.

Idan har shirin Madrid ya tafi yadda take so ƙungiyar za ta cika da matasa kuma haziƙan 'yan kwallo, irin su Aurelien Tchoumameni da Eduardo Camavinga da Jude Bellingham a tsakiyar ƙungiyar. Dan wasan Turkiyyar da Luka Modric sai kuma wa?