You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806446

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Waiwaye: Tinubu ya zama shugaban Ecowas, gurfanar da Emefiele a gaban kotu

Bola Ahmed Tinubu, Nigeria's president- Bola Ahmed Tinubu, Nigeria's president-

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi ranar Lahadi 09 ga watan Yuli zuwa Asabar 15 ga wata.

An zaɓi Tinubu shugaban ƙungiyar Ecowas

A cikin makon da ya gabatan ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya zama shugaban ƙungiyar Economic Community of West African States (Ecowas) ta ƙasashen Afirka ta Yamma.

An zaɓi shugaba Tinubu - wanda ya maye gurbin Shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Embalo - a taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar karo na 63 da aka gudanar a Guinea-Bissau.

"Za mu ɗauki dimokuraɗiyya da muhimmanci. Tana da wuya amma ita ce tsarin gwamnati mafi dacewa," a cewar Tinubu bayan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar.

Wannan ne taro na biyu da shugaban na Najeriya ke halarta a ƙasashen waje tun bayan da ya hau mulki a watan Mayu biyo bayan nasarar da ya yi a zaɓen watan Fabrairu.

Baya ga alwashin jagoranci na gari da ya ci, Tinubu ya bayyana damuwa kan yadda "matsalar tsaro da ta'addanci ke mayar da yankin Afirka ta Yamma baya".




DSS ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu

Haka kuma a cikin cikin makon ne hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele a gaban kotun.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunaya ya fitar, ya ce hukumar ta gurfanar da Mista Emefiele a gaban kotun ne domin bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta bayar da ta umarci hukumar ta DDS da kai shi kotu domin tuhumarsa ko kuma ta sake shi.

Sanarwar ta ambato Mista Afunaya na cewa tun shekarar 2022 ne, hukumar DSS ta nemi umarnin kotu domin tsare Emefiele don gudanar da bincike kan wasu manyan laifuka da ka zarge shi da aikatawa.

Ranar Laraba ne dai wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya ta tuhumi Godwin Emefiele a kotu cikin mako ɗaya ko kuma ta sake shi.

Majalisar Dattawa ta amince wa Tinubu ya ciyo bashin $800m

A ranar Alhamsi ne kuma Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar shugaban ƙasar Bola Tinubu ya karɓo rancen dala miliyan 800 don gudanar da shirin samar da tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

Haka kuma Majalisar ta yi gyara fuska ga dokar ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2022.

Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto buƙatar shugaban ƙasar cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar.

Tinubu ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasar Muhammdu Buhari ta amince da karɓo ƙarin rancen na dala miliyan 800 daga Bankin Duniya, domin aiwatar da shirin tallafin.

Shugaban ya ce maƙasudin shirin, shi ne domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi don su samu abin biyan buƙataunsu na rayuwa.

Shawarar da gwamnonin PDP suka yanke kan matsalolin Najeriya

Yayin da ake ganin matsaloli na ƙara dabaibaye babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, 'ya'yan jam'iyyar na ci gaba da fadi-tashin nemo bakin zaren matsalolinsu.

Kan haka ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar hamayya ta PDP ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa da kuma samun matsaya kan inda jam'iyyar ke neman dosa.

Wannan ne taro na farko da ƙungiyar ta yi irin wannan taro, tun bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka yi, kuma ya gudana ne a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

An tattauna manyan ƙalubalen da jam'iyyar take fuskanta waɗanda suka ƙi bayyana wa 'yan jarida, suna cewa hakan bayyana lago ne ga abokan hammaya, in ji shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad.

Danna nan domin karanta cikakken labarin

Zulum ya dakatar da ayyukan ƴan jari-bola a Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zullum, ya dakatar da ayyukan 'yan jari bola a sassan jihar.

Gwamnan ya dauki matakin ne da nufin kare irin wadannan masu sana'a da ci gaba da kashe su da 'yan Boko Haram ke yi a wajen garuruwan kananan hukumomin jihar.

Ba a san adadin matasan da ke irin wannan sana'a da ke tafiye-tafiye zuwa garuruwa don sana'arsu da aka kashe ba.

Da yake sanar da matakin, Gwamna Zullum, ya ce," A cikin shekaru biyar da suka wuce, an kashe mutane da dama a sakamakon yawan jari-bola da suke abin da ya janyo gwamnatin jihar ta fara bincike a kai ke nan."

Ya kara da cewa, " Kuna ganin wannan wajen, duk waje ne mallakin gwamnati, sannan daga baya kuma waje ne mallakin kamfanonin sadarwa.

A don haka irin wadannan sana'o'i zagon-kasa ne da ake yi wa gwamnatin tarayya, a don haka na bayar da umarnin dakatar da wannan sana'a."

Abba ya mayar da Sheikh Daurawa kan shugabancin Hisba ta Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan muƙamin shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano.

A lokacin da yake tabbatar da komawa kan muƙamin ga BBC, Sheikh Daurawa ya ce: "Lallai a yau na je ofishin SSG na kaɓo takardar kama aiki."

A watan Mayun 2019 ne Sheikh Daurawa, tare da wasu jami'an hukumar ta Hisba a wancan lokaci suka ajiye muƙamansu.

Duk da dai babu cikakken bayani kan dalilin ajiye aikin nasa a wancan lokaci, an yi amannar cewa hakan ya faru ne sanadiyyar rashin jituwa tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

A tattaunawar tasa da BBC, Sheikh Daurawa ya ce ya sake karɓar muƙamin ne kasancewar gwamnatin ta yanzu "Sun nuna min cewa da gaske suke yi, sun nuna min cewa da gaske za su yi aiki."

Ya ƙara da cewa: "Dalilin da ya sa na ajiye aikin a baya shi ne saboda aikin yaƙi yiwuwa daga ƙarshe-ƙarshe."

'Abin da zan mayar da hankali a kai'

A tattaunawar tasa da BBC, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce babban abin da zai mayar da hakali a kai shi ne batun auren zawarawa, kamar yadda gwamnan jihar ya alƙawurta.

Ya ce "Gwamnan a cikin kamfe ɗinsa ya ce zai aurar da zawarawa da ƴanmata da kuma taimaka wa harkar iyali da marayu da kuma iyayen marayu, waɗanda aka mutu aka bar su da yara. Shi ne abu na farko da za mu sa a gaba."

Ya kuma ce zai ɗora a kan abubuwa masu kyau da aka yi a Hisbah tare kuma da duba inda za a yi gyara.

Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci kan samar da abinci

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan batun samar da abinci a ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin mayar da duka al'amuran da suka shafi samar da abinci da ruwan sha, a matsayin manyan abubuwan dogaron rayuwa zuwa ƙarƙashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.

Alake ya ce umarnin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na tabbatar da tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

Ya ce Shugaban ya damu kan yadda farashin kayan abinci ke ƙaruwa da yadda hakan ke shafar talakawan ƙasar.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin gaggauta bai wa manoman ƙasar taki da irin shuka domin rage musu raɗadin cire tallafin man fetur.

Ya ƙara da cewa “Dole hukumomin ayyukan gona da ta ruwan sha su yi aiki tare domin tabbatar da ingantuwar noman rani a ƙasar don tabbatar da samar wadataccen abinci a ƙasar a kowanne yanayin shekara''.

NCAA ta dakatar da jiragen Max Air ƙirar Boeing 737 daga aiki

Hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Najeriya NCAA ta ce ta dakatar da ayyukan jirgin sama na Max Air ƙirar Boeing 737 nan take.

Da take bayyana dakatarwar a cikin wata sanarwa, Daraktan kula da Ayyuka da Horaswa da kuma ba da Lasisi, Kyaftin Ibrahim Dambazau da kuma Babban Daraktan Hukumar Kyaftin Musa Nuhu suka fitar, hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu al'amura da suka faru da jiragen Max Air ƙirar B737.

A cikin wasikar, hukumar ta NCAA ta lissafa abubuwan da suka faru waɗanda har suka sanya ta ɗaukar wannan mataki.

A ciki har da lalacewar wilin tayar saukar jirgi ta gaba, da ta janyo wani mummunan al'amari ga jirgin Boeing 737-400 tsakanin tashinsa daga filin jirgin sama a jihar Adamawa zuwa saukarsa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe a Abuja ranar 7 ga Mayu, 2023.

Hukumar NCAA ta sake soke tashin jirgin Max ƙirar Boeing 737-400 mai lamba 5N-MBD a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) saboda fitar iskar gas mai tsananin zafin a jirgin ranar 11 ga Yuli, 2023.

NCAA ta kuma cewa ta kafa wata ayarin jami'an bincike da za su bi diddigi game da harkokin kamfanin na Max Air.

Hukumar ta ce dole sai sun gamsu da sakamakon binciken, kafin ta bai jirgin Boeing 737-400 damar ci gaba da ayyukansa.