You are here: HomeAfricaBBC2023 09 05Article 1837832

BBC Hausa of Tuesday, 5 September 2023

Source: BBC

Waiwaye : Rikicin NNPP da rabon tallafin rage raɗaɗi

Sanata Rabiu Musah Kwankwaso, shugaban jamiyyar NNPP Sanata Rabiu Musah Kwankwaso, shugaban jamiyyar NNPP

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke ban kwana da shi

Babu wanda ya isa ya kori Kwankwaso daga NNPP - Buba Galadima

A makon da muke ban kwana da shi ɗin ne wani tsagin jam'iyyar NNPP mai mubaya'a ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sanar da korar ƴan kwamitin amintattun da suka dakatar da jagoran jam'iyyar.

Ɗaya daga cikin jigo a jam'iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a wani yunkurin na fasalta al'amuran jam'iyyar.

Wannan mataki na zuwa ne bayan a ranar Talata aka samu labarin da ke cewa NNPP ta dakatar da Kwankwaso kan zargin yi wa jam'iyyar zangon-kasa.

Sai dai Injiniya Galadima ya ce sun yi mamakin jin labarin dakatar da Kwankwaso saboda su ne kwamitin amintattun, kuma ba su san da zaman rassan jam'iyyar da ke cewa sun dakatar da Kwankwaso ba.

Karanta cikakken labarin a nan

Rabon tallafi ya haifar da tashin farashin shinkafa a Najeriya

Matakin da gwamnatin Tarayyar Najeriya da jahohi ke ɗauka na sayen kayan abinci domin rarrabawa a matsayin tallafi ya haifar da tashi kayan abinci a kasuwanni.

Rahotanni na nuna cewa 'yan kasuwa da dama na bayyana cewa buƙatar sayen kayan abincin da masu kwangila ke daɗa yi shi ne ya haifar da wannan lamari, ga shi kuma an samu ƙarancin shigo da abinci a kasuwanni.

Tun bayan da Hukumar da ke lura da tattalin arzikin Najeriya ta fitar da sanarwa a ranar 7 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta amince a fitar da naira biliyan 5 domin sayen abincin da za a tallafawa talakawa, aka soma faɗawa wannan yanayi.

Gwamnatin ta Najeriya dai ta bayar da umurnin raba buhunan shinkafa ga dukan jihohi 36 domin rage raɗaɗin talaucin da 'yan ƙasar suka shiga sakamakon cire tallafin mai.

Tinubu ya ware naira biliyan 50 don aikin sake gina yankunan arewa - Kashim Shettima

A ranar Alhamis ne mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima, ya ce shugaban ƙasar ya ware naira biliyan 50 don aikin sake gina yankuna arewa maso yamma da arewa maso gabashin ƙasar, da ke ci gaba da gudana.

Sanata Shettima ya ce matakin wani yunƙuri ne na magance matsalar tsaro da yankunan ke fama da ita.

Yana wannan jawabin ne a lokacin da Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addinin Musulunci - ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar lll - ta kai ziyara fadar shugaban ƙasar cikin makon da ya gabatan.

Tun da farko shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da ke haifar da matsin rayuwa da gwamnatinsu ke yi, sakamakon cire tallafin man fetur za su amfani 'yan ƙasar da dama a nan gaba.

'Rundunar 'yan sandan Najeriya na buƙatar ƙarin jami'ai 190,000 don kawar da laifuka'

Haka kuma a dai makon da ya gabatan ne Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun ya ce rashin isassun 'yan sanda, na kawo wa rundunarsu tarnaƙi wajen daƙile aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Da yake gabatar muƙala - ga manyan jami'ai masu halartar kwas na 45 a cibiyar tsara manufofi da dabarun shugabanci ta Kuru a jihar Filato - Mista Egbetokun ya ce rundunar na buƙatar ƙarin 'yan sanda 190,000 domin tabbatar da ayyukanta na tsaron rayuka da dukiyar al'umma a cikin gida.

Ya ce a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta tanadi cewa kamata ya yi ɗan sanda ɗaya ya kula da mutum 460, a Najeriya ɗan sanda ɗaya na kula da mutum 650 ne.

Karanta cikakken labarin a nan

'Yan majalisa sun fusata kan kashe naira biliyan 81 wajen dashen itatuwa a Arewa

Hukumar kula da shirin dashen itatuwa wanda aka fi sani da Great Green Wall Project na fuskantar bincike kan yadda ake zargin ta kashe naira biliyan 81 domin dashen bishiyoyi miliyan ashirin da ɗaya a jihohin arewa da ke kan iyakar Najeriya.

Kwamitin majalisar wakilan Najeriya ne ke gudanar da binciken, a kan yadda aka yi amfani da asusun raya muhalli da alkinta yanayi da wasu kuɗaɗen asusun.

Jihohin sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauci da Gombe da Adamawa da Yobe da kuma Borno.

Daraktan Hukumar ta NAGWW, Yusuf Maina Bukar, ya shaida wa kwamitin cewa hukumar ta kashe naira miliyan 697.71 wajen gyara ofishinta da kuma naira biliyan 11.28 don gudanar da manyan ayyuka.

Ka cikakken labarin a nan

Gwamnan Katsina ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage raɗaɗi

Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Raɗɗa ya ce ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 nan take, ga al'ummar jihar da nufin rage raɗaɗin matsin rayuwa bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne daga kuɗin rage raɗaɗi da jihar ta karɓa daga gwamnatin tarayya.

Ya kuma ce ya amince da kafa kwamitoci don raba shinkafar a matakan ƙananan hukumomi da mazaɓu na jihar.

Sai dai, saɓanin naira biliyan biyar da Majalisar kula Tattalin Arziƙin Ƙasa ta ambata tun farko bayan wani taro da ta gudanar kwanan baya, Gwamna Umar Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne da naira biliyan biyu da gwamnatin tarayya ta saki.