You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816598

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Waɗanda suka tsira a harin Pakistan sun siffanta lamarin da 'tashin ƙiyama'

Hoton inda harin ɗan ƙunar baƙin-wake ya shafa a Pakistan Hoton inda harin ɗan ƙunar baƙin-wake ya shafa a Pakistan

Mutanen da harin ɗan ƙunar baƙin-wake ya shafa a Pakistan sun bayyana da lamarin da mai kama da "tashin alƙiyama", kamar yadda suka shaida wa BBC.

Tashin hankalin ya faru ne bayan maharin ya tashi bam ɗin da ke jikinsa a wurin taron siyasa, inda ya kashe aƙalla mutum 45 ranar Lahadi.

Mutane sun yi ta ihun neman taimako yayin da masu ba da agaji suka bazama zuwa gundunamr Bajaur da ke arewa maso yammacin ƙasar, a cewar wanda ya shirya gangamin mai suna Imran Mahir.

An kai wa jam'iyyar Jamiat Ulema-e-Islam-Fazl (JUI-F) harin, wadda ke cikin haɗakar jam'iyyun da ke kan mulki.

"Mutumin da ke gefena ya mutu, ɗayan kuma ya ji rauni," in ji Mista Mahir.

"Babbar ƙara na ji. Da farko ma na zaci janareton ne ya samu matsala, ko kuma lasifika. Har yanzu kunnuwana na kaɗawa da ciwo. Kaina har yanzu ciwo."

Ɗaruruwan magoya baya ne suka taru a matsayin wata dama da jam'iyyar mai ra'ayin Musulunci ta samu don nuna kwarjininta gabanin zaɓen da za a yi a shekarar nan.

Mista Mahir da ke kan wani dandamali lokacin da bam ɗin ya fashe, ya bayyana yadda fashewar ta haddasa gobara da kuma turniƙewar hayaƙi a saman garin Kharda ke lardin Khyber Pakhtunkhwa wanda ke da kusa da iykar Pakistan da Afghanistan.

"Na ga matattu da waɗanda aka jikkata a kwance. Lamrin ya munana sosai - kamar tashin ƙiyama. Sai kuma aka shiga fargaba bayan fashewar, mutane na ta karakaina a wurin," in ji shi.

"Ban san ya aka yi ban ji rauni ba, na yi sa'a wa'adina bai cika ba tukunna. Akwai wani mai shekara 80 da ke da nisa da bam ɗin, amma ya rasu," kamar yadda ya bayyana.

Hukumomi sun yi gargaɗin cewa adadin waɗanda aka kashe zai iya ƙruwa, yayin da mutum 15 suka ji munanan raunuka.

Wani shugaban yanki na JUI-F, Maulana Ziaullah, na cikin waɗanda suka rasu, kamar yadda shugabannin yankin suka shaida wa BBC.

"Ba mu taɓa tunanin hakan za ta faru da 'yan siyasa ba ko ɗalibai. Ba mu taɓa tunanin haka ba, ba ma kawo hakan a ranmu," a cewar Mahir.

Ya ce ya halarci jana'izar mutum bakwai cikin dare.

Sai dai ya ce gwiwar 'yan JUI-F ba ta sanyaya ba, tana nan "a ƙarfafe", in ji shi. "Ba za mu saurara ba wajen neman kujerun majalisa, za mu ci gaba. Hankalinmu na tunanin gaba ne."

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi tir da harin kuma ya siffanta waɗanda suka kai shi a matsayin 'yan ta'adda masu kai wa "mutanen da ke kare Musulunci da Ƙur'ani da Pakistani hari". Ya ce za su fuskanci "hukunci mai tsauri".

Yayin da har yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin, reshen ƙungiyar IS a Pakistan ya sha ɗaukar alhakin kai wasu hare-hare a wanna shekarar, har ta taɓa kai wa jam'iyyar JUI-F hari.

A watan Yuni, ƙungiyar ta ce ita ta kashe jami'in wata jam'iyya a ƙauyen Inayat Killi.

Ƙungiyar Pakistani Taliban (TTP) ta yi tir da harin kuma ta nesanta kanta da shi.