You are here: HomeAfricaBBC2022 10 14Article 1642940

BBC Hausa of Friday, 14 October 2022

Source: BBC

Wolves na zawarcin tsohon kocin da ta kora Nuno Espirito

Nuno Espirito Santo Nuno Espirito Santo

Kungiyar Wolves na tattaunawa da tsohon kocinta Nuno Espirito Santo domin ya koma aikin koyar da kungiyar ta Molineux. Kungiyar na gudanar da wani aikin daukar ma'aikata bayan Spaniard Julen Lopetegui ya ki karbar aikin horas da kungiyar. Nuno dan kasar Portugal an kore shi kai tsaye ne a 2021 bayan wuyar da ya sha a wannan kakar inda kungiyar ta kare a matsayi na bakwai. Magoya bayan Wolves na matukar son shi duk da horar da Tottenham da ya yi na dan karamin lokaci. A watan Nuwambar bara ne Spurs ta korin kocin mai shekara 48 bayam buga wasa 17 cikin watanni hudu. A Yuli aka nada shi kocin kungiyar Saudiyya ta Al-Ittihad kan kwantaragin shekara biyu. Abin da ya kara daga mutuncin Nuno a Wolves shi ne daga likafarta da ya yi zuwa gasar Premier a shekararsa ta farko ta horas da kungiyar. Wolves na cikin kungiyoyi ukun karshe na tawagar Premeir nasara daya kacal ta yi a wasa tara da ta buga a kakar nan.