You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1854035

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Victor Osimhen: Watakila ɗan Najeriya zai kai ƙarar Napoli

Victor Osimhen Victor Osimhen

Wakilin ɗan kwallon Najeriya, Victor Osimhen – Roberto Calenda ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a a kan ƙungiyar Napoli bayan da kulob ɗin ya yi wa ɗan wasan shaguɓe a soshiyal midiya.

A shafin Tiktok, kungiyar Napoli ta wallafa bidiyon lokacin da Osimhen ya ɓarar da bugun fenariti a wasansu da Bologna.

Daga baya ƙungiyar ta goge bidiyon.

“Muna da ƴancin ɗaukar matakin shari’a domin kare Victor,” in ji Calenda.

“Abin da ya faru a shafin Napoli na Tiktok ba za mu yarda da shi ba”.

An ga Osimhen a bidiyon yana ƙalubalantar kocinsa Rydu Garcia, lokacin da aka cire shi a wasan a minti na 86 wanda suka tashi babu ci tsakaninsu da Bologna.

Dan kwallon Najeriyar ya koma Napoli ne a kan Euro miliyan 81.3 a bazarar 2020 kuma yana cikin tawagar da ta taimaka wa ƙungiyar lashe gasar Serie A a karon farko cikin shekaru 33 inda ya ci kwallo 26 a wasa 32.

A lokacin musayar ƴan ƙwallo, an yi ta alakanta Osimhen da komawa Chelsea ko Manchester United domin murza leda a can.