You are here: HomeAfricaBBC2023 12 14Article 1898132

BBC Hausa of Thursday, 14 December 2023

Source: BBC

Victor Osimhen: Daga ɗan talla kan titi a Lagos zuwa 'sabon sarki a Afirka'

Victor Osimhen Victor Osimhen

Ana jinjina wa "sabon sarki a Afirka," Victor Osimhen bayan an bayyana sunan ɗan wasan gaban na Najeriya, a matsayin Gwarzon Ɗan ƙwallon nahiyar na Shekara ta 2023.

Ɗan ƙwallon na kulob ɗin Napoli mai shekara 24, ya karɓi wannan lambar yabo ne a daren Litinin, yayin bikin ba da lambobin karramawa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Aifrka (Caf), inda ya murƙushe hamayyar abokan karawarsa kamar kyaftin ɗin Masar Mohamed Salah da ɗan bayan Moroko Achraf Hakimi.

Ga Osimhen, wanda ya taso a titunan turɓaya na unguwar Olusosun cikin birnin Lagos, wannan wani "cikar burin rayuwa" ne bayan ya fuskanci tsananin gargada a lokacin yarintarsa.

"Ina miƙa godiyata ga kowa da kowa da ya taimaka mini a wannan tafiya, da kuma duk 'yan Afirka da suka taimaka wajen ɗora ni kan wannan matsayi duk da matsalolina," cewar Osimhen.

Osimhen wanda a kullum ɗoyin tarin bola yake yi masa sallama a unguwarsu, ya ce yana da maitar burin cimma nasara, duk da ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwa.

Sai da ya yi tallan jarida, kuma ya yi sana'ar sayar da ruwan roba, lamarin da ya bayyana da kasancewa a halin "rayuwa mafi wahala".

"A matsayina na yaron da ya taso yana talla a tsakanin motoci a kan titi kusan a kullum, don kuɓuta daga ɗumbin ƙalubalen da ni da iyayena muka yi fama da shi, zamowa mai irin wannan daraja a Afirka da ma duniyar ƙwallon ƙafa, wani katafaren buri ne a gare ni," ya rubuta cikin wani saƙo a dandalin X.

"Gwagwarmayar ƙwallon ƙafata, ta kasance wani lilo mai hawa da gangara cike da gargada da kuma shauƙi."

"Cikar buri da murnar nasarori ne suka riƙa yi min ƙaimi, hatta a lokacin da masu suka da nuna ƙiyayya da zafin kaye suka riƙa bugun ƙirjina da ƙarfi."

Bayan ya ci ƙwallo 26 ne ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Serie A ta farko a cikin shekara 33, Osimhen ya zama ɗan Najeriya na ɗaya da ya ci lambar karramawa ta Caf a ɓangaren maza tun bayan tsohon ɗan wasan gaban Arsenal, Nwankwo Kanu a 1999.

"Abin da Osimhen ya yi ya fi ƙarfin hankali," in ji tsohon ɗan ƙwallon Arsenal daga ƙasar Togo Emmanuel Adebayor, wanda ya lashe irin wannan lambar yabo ta Afirka a 2008.

"Cin ƙwallaye mai yiwuwa abu ne mai sauƙi a Ingila amma yin haka a Italiya ba mai sauƙi ba ne saboda suna ƙarfi a wajen tsare baya da kuma tsara dabarun wasa."

Yayin da shi kansa tsohon ɗan wasan gaban Ivory Coast Didier Drogba, wanda sau biyu yana ɗaukar lambar lambar Caf ta Gwarzon Afirka na Shekara, ya bayyana tsohon ɗan wasan gaban Lille a matsayin sabon sarkin ƙwallon ƙafan Afirka, kuma yanzu akwai kyakkyawan fatan cewa zai ingiza Najeriya zuwa ga wani sabon zangon nasara.

Yaro mai nasibi

Tasowar Osimhen zuwa ganiya, abu ne da ya ɗauki lokaci sannu a hankali maimakon labarin abin mamaki na kakar wasanni ɗaya.

Kasancewarsa tauraro ga Najeriya a nasararsu ta cin Kofin Duniya na 'yan ƙasa da shekara 17 a 2015, wani muhimmin lokaci ne a sana'arsa wadda ta nuna shi yaro ne mai nasibi.

Ƙwallo 10 da ya ci a Chile ta ba shi damar samun kyautar takalmin zinare kuma Caf ta bayyana sunansa a matsayin Matashin Ɗan wasa na Shekara - duk da haka Osimhen ya kusan rasa damar shiga sahun 'yan wasan da aka ɗauka.

"Ai tuni hankalina ya tafi daga kansa saboda an riƙa haɗa shi da wasu 'yan wasa waɗanda ba su taɓuka abin kirki ba," Emmanuel Amuneke, kociin ƙungiyar ya faɗa wa Sashen Wasanni na BBC Afirka.

"Amma jami'an da ke tallafa min sun lura da shi kuma suka ja hankalina gare shi. Ni kuma na sake ba shi dama don ya fito da kansa ta yadda zai iya shiga sahun 'yan wasan farko."

Ba abin mamaki ba ne da Osimhen, bayan karɓar lambar yabonsa ta Caf a Moroko, ya ɗauki lokaci wajen yabawa tsohon kocinsa saboda taimaka masa da ya yi har ya cika burinsa.

"Godiya ta musamman ga Emmanuel Amuneke. Ba don shi ba, ba na jin zan tsaya nan a gabanku balle har na riƙe ɗaya daga cikin lambobin karramawa mafi daraja a duniyar ƙwallon ƙafa," ya ce.

Tabbas akwai gargada ƙalilan a kan hanyarsa ta samun nasara.

Tafiyarsa zuwa kulob ɗin Wolfsburg na Jamus a watan Janairun 2017 ta kusan zama mugun mafarki ga burin matashin ɗan ƙwallon, wanda ya buga wasa 16 ba tare da ya ci ko ƙwallo ɗaya ba, kafin tafiyarsa aro zuwa ƙungiyar Charleroi ta Belgium a tsakanin 2018-19, ta buɗe ƙofa.

Shaharar Osimhen ta kai ta kawo a Lille, inda har aka ba da rahoton cewa Napoli sun biya dala miliyan 96 a kan ɗan wasan - wanda ya zama kuɗi mafi tsada da aka taɓa sayen wani ɗan ƙwallon Afirka - saboda ƙoƙarinsa a watan Yulin 2020.

Kafin mashahuriyar kakar wasanninsa wadda ya lashe gasar tarihi ta Serie A, ala dole ya gaza samun damar buga Gasar cin Kofin Afirka ta 2021 (Afcon) saboda annobar korona da wani rauni da ya ji a fuska wanda har yanzu sai ya sanya abin kare fuska don yin wasa.

Bugu da ƙari, ga kuma mutuwar mahaifi da mahaifiyarsa a 2020.

"Rasa iyayena abin ƙaunata a lokacin da nake wannan gwagwarmaya, abu ne da ya bar wani tabo a zuciyata, saboda a ko da yaushe sun kasance wani doron samun ƙwarin gwiwar nasarata," Osimhen ya ƙara da cewa a saƙonsa na shafin X.

"Ga iyalina abin alfaharina, ina gode muku a ko da yaushe saboda goyon bayanku da kuma ƙaunar da kuke nuna min. Da babu goyon bayanku, da ban kawo wannan matsayi ba."

Wani sabon zamani ga ƙwallon ƙafar Afirka?

Ɗan wasan gaban Liverpool Salah da tsohon abokin na kulob ɗin Reds Sadio Mane, dukkansu 'yan shekara 31, sun lashe lambar yabo ta Caf guda huɗu a tsakaninsu, to ko nasarar Osimhen a birnin Marrakesh za ta bijiro da zuwa sabbin matasa 'yan zamani ne.

Takwaransa na ƙungiyar Super Eagle Victor Boniface da ke buga wa kulob ɗin Bayer Leverkusen, da ɗan wasan tsakiyar Ghana Mohammed Kudus na kulob ɗin West Ham da ɗan wasan gaba na ƙasar Guinea Serhou Guirassy da ke ƙungiyar Stuttgart dukkansu tuni suka yi amo a wannan kakar wasanni.

Yayin da magoya bayan Najeriya ke fatan lambar karramawar da Osimhen ya ci za ta samar da ƙwarfin gwiwa ga ƙasar ta sake ƙalubalantar ɗauko Kofin Afirka , wanda rabon ƙasar ta Afirka ta Yamma ta ɗauka tun a shekara ta 2013.

Super Eagles ta gaza samun cancantar zuwa gasar cin kofin Afirka a 2015 da kuma a 2017, sannan ta ƙare a matsayi na uku a 2019, yayin da aka fitar da ita a rukunin sili-ɗaya-ƙwale a karon da aka buga gasar a Kamaru cikin 2021.

"Wannan karramawa a mataki mafi girma wata gagarumar ƙarfafa gwiwa ce ga ƙwallon ƙafan Najeriya, shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Adam Muktar Mohammed ya faɗa wa AFP.

"A bayyane take, akwai ɗumbin masu baiwar ƙwallon ƙafa a Najeriya. Kawai abin yi shi ne mu san yadda za mu fito da wannan baiwa don zama gagara-badau a fagen ƙwallon duniya."

Drogba - wanda Osimhen ya bayyana a matsayin tauraronsa lokacin da yake tasowa - ya yi imani Najeriya tabbas za ta iya zama barazana a gasar cin Kofin Afirka ta 2023, wadda za a fara cikin watan gobe a Ivory Coast.