You are here: HomeAfricaBBC2023 02 14Article 1714358

BBC Hausa of Tuesday, 14 February 2023

Source: BBC

Valencia ta nada Baraja sabon kociyanta

Ruben Baraja Ruben Baraja

Kungiyar Valencia ta nada tsohon dan wasanta, Ruben Baraja a matakin sabon kociyanta.

Mai shekara 47 shi ne na 10 da kungiyar ta dauka cikin kaka tara.

Ya maye gurbin Gennaru Gattuso, wanda ya bar aikin a watan jiya, bayan wata bakwai yana jan ragama.

Baraja ya buga wa Valencia wasa 364 tsakanin 2000 zuwa 2010 da yi wa tawagar Sifaniya tamaula 43.

Valencia wadda ta yi rashin nasara a wasa shida daga bakwai a La Liga tana ta ukun karshe a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Baraja ya horar da Elche da Rayo Vallecano da Sporting Gijon, da Tenerife da kuma Real Zaragoza.