You are here: HomeAfricaBBC2023 12 07Article 1894580

BBC Hausa of Thursday, 7 December 2023

Source: BBC

'Umurnin da PDP ta bayar zai iya sake tsunduma jam'iyyar cikin rikici'

PDP ce jamiyyar adawa a Najeriya PDP ce jamiyyar adawa a Najeriya

Babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya , wato PDP ta umurci`ya`yanta da suka gurfanar da ita a gaban kuliya sakamakon rigingimun cikin gida, da su janye kararrakin saboda ta samu bude hanyar sulhu da dai-daita tafiyar jam`iyyar da `ya`yan nata.

Kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya ce, kundin tsarin mulkin jam`iyyar ya haramta wa `ya`ya kai mahaifiyarsu kara gaban kuliya.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri wanda mamba ne a Kwamitin Amintattun na jam`iyyar PDP , ya shaida wa BBC cewa dokar dadaddiya ce amma wasu `ya`yan jam'iyyar na mata biyayya ce irin ta ganin dama:

“Ba a kai jam’iyya kara kotu, wanda duk ya kai jam’iyya kara kotu, jam’iyya ta tanadi irin hukuncin da yakamata a yi mi shi, kuma wannan shi ne dai -dai, domin yanzu mu ke bukatar jam’iyyar ta koma bisa kafafunta”

“Idan ka kai karar jam’iyya, ba ta jam’iyyar ka ke yi ba, ta kanka ka ke yi kennan, saboda haka abinda ake so shi ne duk wani abu da ya shafi laifufuka ko kuma jin ba ‘a yi ma dai- dai ba, akwai matakin da jam’iyya ta ce a bi, akwai kwamitin sassanci tun daga rumfar zabe har ya zuwa matakin uwar jam’iyyar , sai an bi wannan a zo karshe”, in ji shi.

Sai dai wasu na ganin umurnin wani sabon salo ne na kama-karya ko tirsasa wa ‘ya’yan jamiyyar PDP amma Sanata Umaru Tsauri ya nanata cewa wannan shi ne tanadin da tsarin mulki ya yi a kan wannan batu kennan:

“Ai tsarin mulki abinda ya ce kennan ayi, shi yasa aka yi mataki iri-iri idan na yi maka laifi ga wurinda za ka kai kara, ko da a irin tarukan nan da ake zabar ‘yan takara, za ka ga cewa duk kwamitin da aka tura, akan tura kwamiti guda biyu ne”, in shi

Sanata Tsauri ya ce akwai kwamitin da ake dora wa alhakin gudanar da zabe akwai kuma akwai kwamitin da za a tura ya je ya saurari kararrakin wadanda aka yi wa ba dai -dai ba a lokacin zaben.

'Abu ne mai wuya umurnin jam'iyyar PDP ya yi tasiri'

Duk da cewa jam`iyyar PDP na da yakinin cewa umurnin nata zai wanzar da zaman lafiya tsakaninta da `ya`yan nata, wasu masana siyasa a bangare guda kuma na ganin cewa ta yi fargar-jaji har mai faruwa ta faru.

Dr Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja ya shaida wa BBC cewa kamata ya yi a ce tun da farko dokar ta iya hana `ya`yan jam`iyyar PDP zuwa kotu maimakon wannan mataki da take dauka na ba da umurnin janye kara wanda umurni ne da ya ce da wuya `ya`yan jam'iyyar su martaba shi:

“ Ina ga biyayya ga wannan umurni da dan wuya kadan, saboda ita kanta jam’iyyar daga sama har kasa a cikin rudani ta ke. Akwai bangarori daban -daban, akwai hamshakan ‘yan jam’iyya da suke ta rigingimu da juna, saboda haka wadansu su za suyi biris da wannan umurni domin mai yiwa biyayyasu ba ga wadanda suka bayar da umurnin bane”, in ji shi .

Sai dai masanin ya yi gargadin cewa umurnin zai iya sake tsunduma jam’iyyar a cikin wasu rikice-rikice :

" Maimakon a ce wannan umurnin ya kawo mu su masalaha yana mai iya sake tsunduma jam’iyyar a cikin wasu rikice rikice. Idan aka ki YIN biyayya ga wannan umurni zai sake rage kima da kuma rage darajar jam’iyyar" in ji shi.

Rigingimun cikin gida matsala ce da dukkan manyan jam`iyyun siyasa a Najeriya suke fama da ita, wadda ake dangatawa da rashin adalcin da ake zargin jam`iyya ko wasu manyan `ya`yanta na yi wa kanana 'ya'yanta.

Wannan ne ya sa jam`iyyun ke fama da matsalar shugabanci a wasu jihohin kasar, ciki har da PDP, wadda a zancen da ake yi shugabancinta na tangal-tangal a jihar Anambara, tun 1999, bayan komawar Najeriya ga turbar demokuradiyya.