You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767605

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

Tsugunne ba ta ƙare wa Erdogan ba zaɓen Turkiyya ya je zagaye na biyu

Mista Erdorgan da 'yan adawar ƙasar, Kemal Kilicdaroglu Mista Erdorgan da 'yan adawar ƙasar, Kemal Kilicdaroglu

Hukumar zaɓe a Turkiyya ta sanar da zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, Mista Erdorgan ya gaza samun kashi 50 na ƙuri`un da za su ba shi nasara.

Shugaban hukumar zaɓen ƙasar Ahmet Yener, ya ce za a gudanar da zagayen zaɓe na biyu ranar 28 ga watan Mayu, wato mako biyu mai zuwa kamar yadda doka ta tanada.

Ahmet Yener ya ce sakamakon zagayen farko na zaɓen ya nuna cewa Shugaba Erdogan ya samu kashi 49.51% na ƙuri'un da aka kaɗa.

Shi kuwa, babban jagoran 'yan adawar ƙasar, Kemal Kilicdaroglu, ɗan takarar gamayyar jam'iyyun adawan Turkiyya, ya samu kashi 44.88% na ƙuri'un.

Mutum na uku da ke takarar Sinan Oğan na jam`iyyar NP, ya samu kashi biyar na ƙuri`un, kamar yadda hukumar zaɓen ta bayyana.

Dokar ƙasar ta tanadi cewa dole ne sai ɗan takara ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, kafin a ayyana shi matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

A yanzu dai kallo ya koma tsakanin Erdogan da Mista Kilicdaroglu, kuma hankula sun karkata kan Sinan Ogan bisa rawar da zai iya takawa a zagaye na biyun.

Mista Ogan dai ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi ɗan takarar da yake adawa da jam'iyyar Kurɗawa tare da shirin korar 'yan gudun hijira.

Muna da ƙwarin gwiwa - 'Yan adawa

Jam'iyyar Recep Erdogan ta samu mafi yawan kujerun majalisar dokokin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Turkiyya ya ruwaito.

Jam'iyyun adawar sun kwashe watanni suna ƙoƙarin haɗa ƙarfi wuri guda domin kawo ƙarshen mulkin Erdogan, wanda ke yunƙurin ƙarfafa ikonsa tun bayan yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekara ta 2016.

Zaɓen ya samu fitowar al'umma, inda alkaluman hukumar zaɓen suka nuna yawan fitar masu zaɓe, ya kai kashi 88.80%.

Ƙasashen Yamma sun sanya ido sosai a kan zaɓen, saboda yadda jagoran adawa Kemal Kilicdaroglu ya alƙawarta maido da martabar dimokraɗiyyar ƙasar da kyautata alaƙar Turkiyya da ƙungiyar NATO.

A ɗaya ɓangaren kuma gwamnatin Shugaba Erdogan wadda ke tafiya a kan tushen tsarin Musulunci, ta zargi Ƙasashen Yamma da kitsa makircin kawar da shi daga mulki.

Da safiyar ranar Litinin, Mista Kilicdaroglu ya bayyana a shalkwatar jam'iyyar da ke Ankara tare da abokan ƙawancensa, inda ya ce yana cike da ƙwarin gwiwa.

"Babu shakka za mu yi nasara a zagaye na biyu na zaɓen'', in ji shi.

Mai magana da yawun jam'iyyarsa Faik Oztrak ya jaddada iƙirarin nasa, inda ya ce jam'iyyar za ta yi abin da ya kamata don shirya wa zagaye na biyu, nan da mako biyu mai zuwa.

Magoya bayansa da ke wajen shalkwatar jam'iyyar sun riƙa waƙe-waƙe tare da kiran taken jam'iyyar, domin nuna goyn bayansu ga Mista Kilicdaroglu.

A baya, Kilicdaroglu mai shekara 74, ya sha faɗuwa zaɓe a jam'iyyar tasa, to amma akwai alamu ƙanshin nasara a kiraye-kirayen da yake yi na kawo ƙarshen ƙarfin ikon da Erdogan ke da shi.

Al'ummar Turkiyya na fama da matsalar hauhawar farashi, wanda a yanzu ya kashi 44 %, mataki mafi muni da ya taɓa kai wa a ƙarƙashin mulkin Erdogan.

Haka kuma an zargi gwamnatin Erdogan da jan ƙafa wajen ayyukan ceto waɗanda girgizar ƙasar ta ritsa da su a watan Fabrairu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 50,000 a lardi 11 na ƙasar.

To sai dai duk da haka, Mista Erdogan ya samu ƙuri'u masu yawa a lardunan.

Sakamakon zaɓen ya nuna cewa goyon bayan Recep Erdogan a larduna takwas da suka fuskanci girgizar ƙasar, ya ragu daga maki uku zuwa biyu.

A birane bakwai daga cikin takwas, goyon bayansa ya kai kashi 60%, a Gaziantep ne goyon bayansa ke kashi 59 cikin 100.

A halin yanzu kallo ya koma kan ɗan takara na uku Mista Sinan Ogan wanda ya ke da kashi biyar na magoya baya.