You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826918

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

Tsohon golan Newcastle ya koma Luton

Luton Town ta dauki golan Netherlands Tim Krul daga Norwich City Luton Town ta dauki golan Netherlands Tim Krul daga Norwich City

Luton Town ta dauki golan Netherlands Tim Krul daga Norwich City.

Krul, mai shekaru 35, ya zama sabon dan wasa na 10 da sabbin shiga gasar Premier suka dauko a bana.

Ya bar kungiyar ta Carrow Road bayan kakar wasa biyar, inda ya buga wasa 169, ya kuma lashe gasar Championship sau biyu.

Sakamakon tafiyar Krul, Norwich ta kawo George Long da ya zo a kyauta daga Millwall.

Krul, wanda ya buga wa kasarsa wasa sau 15, zai kawo kwarewar buga gasar Premier zuwa Luton, inda a baya ya shafe shekaru shida tare da Newcastle United.