You are here: HomeAfricaBBC2023 08 07Article 1820207

BBC Hausa of Monday, 7 August 2023

Source: BBC

Tottenham ta yi watsi da sabon tayin Bayern kan Kane

Harry Kane Harry Kane

Tottenham ta ki amincewa da sabon tayin da Bayern Munich ta yi wa dan wasanta na gaba Harry Kane.

Bayern ta yi fatan cimma yarjejeniya kan sayen kyaftin din Ingila, amma an fahimci bangarorin biyu ba su daidaita kan darajar dan wasan mai shekaru 30 ba.

Zakarun Bundesliga sun nuna cewa idan tayin da suka yi na Kane bai yi nasara ba a wannan karon za su hakura da zawarcin dan wasan.

Sai dai yayin da ya rage mako uku a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa, sai dai a jira a gani ko kungiyar za ta hakura.

Kane, wanda ya zira kwallaye 280 a wasanni 435 da ya buga wa Tottenham a dukkan wasanni, ya jagoranci 'yan wasanta a wasan da suka yi da Shakhtar Donetsk a ranar Lahadi.

Shekara daya ta rage a yarjejeniyarsa da Tottenham kuma babu alamun Kane na son tsawaita kwantiragin.

Idan shugaban kungiyar Daniel Levy ya zabi ci gaba da rike dan wasan na Ingila hakan zai kawo karshen dama ta karshe da kungiyar za ta iya samun kudi a kansa, saboda zai bar ta kyauta a ƙarshen kaka mai zuwa.

Jami'an Bayern sun gana da Levy a makon da ya gabata amma ba a cimma matsaya ba.

Tottenham za ta fara gasar Premier bana a Brentford ranar 13 ga Agusta. Yayin da Bayern za ta fara kakar wasan ta da RB Leipzig a gasar Bundesliga ranar 12 ga watan Augusta.

Za a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa ranar 1 ga watan Satumba, amma bangarorin biyu sun fi son a kulla yarjejeniya kafin a fara sabon kakar wasa.