You are here: HomeAfricaBBC2023 09 01Article 1836302

BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Tottenham ta ƙulla yarjejeniya da Forest kan Johnson

Brennan Johnson Brennan Johnson

Tottenham ta amince ta biya sama da fam miliyan 45 don siyan Brennan Johnson daga Nottingham Forest.

Yanzu ɗan wasan na Wales na shirin zama dan wasan Spurs na tara a bazarar nan.

Johnson wanda ya fara wasa a bangaren matasan Forest ya zura kwallaye 29 kuma ya taimaka aka zura 12 a cikin manyan wasanni 108 da ya buga.

Kungiyar Spurs ta Postecoglou ta samu maki bakwai a wasanni uku na farko na gasar Premier.

Zuwan Johnson zai taimaka wajen cike gurbin da aka samu a ƙungiyar bayan Harry Kane ya koma Bayern Munich a watan jiya.