You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853921

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Tottenham ta taka wa Liverpool burki bayan wasa 17 ba a doke ta ba

Hoto daga gasar Hoto daga gasar

Tottenham ta doke Liverpool da ci 2-1 a wasan mako na bakwai a gasar Premier League da suka kara ranar Asabar.

A minti na 36 Tottenham ta ci kwallo ta hannun Heung-min Son, karo na hudu kenan da yake cin Liverpool a karawa da su.

Daga baye ne Liverpool ta farke ta hannun Cody Gakpo daf da za su je hutun rabin lokaci.

Tun kan a ci Liverpool aka bai wa dan wasanta, Curtis Jones, jan kati a minti na 26 da take leda.

Karo na uku kenan da ake bai wa dan kwallon Liverpool jan kati a wasa bayan wanda aka yiwa Mac Allister a karawa da Bournemouth da Virgil van Dijk a wasan Tottenham.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne aka kara bai wa Liverpool jan kati na biyu a fafatawar, inda aka kori Diogo Jota.

Daf da za a tashi wasa ne Liverpool ta ci gida ta hannun Joel Matip, da hakan ya bai wa Tottenham maki ukun da take bukata.

Karon farko da aka ci Liverpool bayan wasa 17 a jere ba tare da rashin nasara ba tun daga Afirilun bara da cin wasa 12 da canjaras biyar.

Tun kan ta ziyarci Tottenham, kungiyar Anfield ta yi nasara a wasa bakwai a jere a dukkan fafatawa da cin kwallo 20.

Ange Postaglou ya ja ragamar wasa 41 kenan a gida ba tare da an doke shi ba a Celtic da Tottenham da cin 35 da canjars shida.

Karo na uku da Tottenham ta yi wasa bakwai da fara Premier ba tare da rashin nasara ba, bayan da ta yi fafatawa 12 a 2016/17.

Ko a bara Tottenham ta yi karawa bakwai ba tare da an doke ta ba a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba, Liverpool za ta karbi bakuncin Union St Gilloise a wasa na biyu a cikin rukuni a Europa League.

Daga nan kuma za ta ziyarci Brighton ranar 8 ga watan Oktoba a wasan mako na takwas a Premier League.

Ita kuwa Tottenham, wadda ba ta buga gasar zakarun Turai a bana za ta karbi bakuncin Fulham a karawar mako na takwas a Premier ranar Litinin 23 ga watan Oktoba.

Sannan ta ziyarci Crystal Palace a fafatawar mako na tara ranar 27 ga watan Oktoba a babbar gasar tamaula ta Ingila.