You are here: HomeAfricaBBC2023 02 19Article 1717373

BBC Hausa of Sunday, 19 February 2023

Source: BBC

Tottenham na zawarcin Antonio Rudiger, Man U na shirin yi wa David de Gea karin albashi

Antonio Rudiger Antonio Rudiger

Tottenham na zawarcin dan wasan Real Madrid da Jamus, Antonio Rudiger, 29, a bazara. (Fijaches - in Spanish)

Manchester United na shirin yi wa David de Gea karin albashi zuwa £250,000 duk mako domin ganin golan na Spaniya mai shekara 32 ya ci gaba da zama a Old Trafford sai dai tuni kungiyar ke hangen golan Leeds Illan Meslier, 22, a matsayin wanda zai maye gurbinsa. (Sun)

Tayin sayen Manchester United da Sir Jim Ratcliffe ya yi kasa yake da tayin Sheikh Jassim Bin Hamad Al Thani ya yi na £5bn. (Foot Mercato - in French)

West Ham za ta yi tayin sayen dan wasan Manchester United Scott McTominay da dan wasan Ingila Harry Maguire, 29 da mai buga wa Netherlands tsakiya Donny van de Beek, 25, da kuma dan wasan gaba na Faransa Anthony Martial, 27. (CaughtOffside)

Hammers din na zawarcin Lazio da mai buga wa Serbia tsakiya Sergej Milinkovic-Savic, 27, cikin yan wasan da za su maye gurbin Declan Rice, idan dan wasan mai shekara 24 ya bar kulob din a bazara. (Sun)

Masu hannun jari na Qatar za su iya neman hannun jari a Tottenham, ko da Sheikh Jassim Bin Hamad Al Thani ya kammala sayen Manchester United. (Times - subscription required)

Manchester City na shirin soma tattaunawa da Julian Alvarez na Argentina game da sabunta kwantiraginsa duk da cewa dan wasan mai shekara 23 ya isa kulob din a bazarar da ta gabata. (Mirror)

Barcelona ta amince ta sayi dan wasan Atletico Madrid da Portugal Joao Felix a Janairun 2022, sai dai yarjejeniyar ba ta tabbata ba saboda dokokin hukumar kula da kudaden da kulob-kulob ke kashewa wato FFP. (AS - in Spanish)

Blackburn Rovers sun yi wa dan wasan Chile Ben Brereton Diaz, 23, tayin £30,000 duk mako tsawon shekara daya domin ya ci gaba da zama da su dai-dai lokacin da Villareal ke zawarcinsa. (Sun)

Newcastle United na shirin sayen dan wasan Fulham da Amurka, Antonee Robinson, 25. (Football Insider)

Dan wasan Nottingham Forest Lewis O'Brien, 24, ya ja hankalin kungiyoyi kamar New York City da Columbus Crew da kuma Atlanta United. (Sun)

Liverpool ta soma tattaunawar farko kan sayen dan wasan Colombia na yan kasa da shekara 20, Kevin Mantilla, 19, daga Independiente Santa Fe. (Football Insider)

Crystal Palace da West Ham sun nuna sha'awar sayen dan wasan Bristol City mai shekara 19, Alex Scott, wanda aka kiyasta farashinsa kan £20m. (Sun)