You are here: HomeAfricaBBC2021 04 16Article 1234342

BBC Hausa of Friday, 16 April 2021

Source: BBC

Tokyo 2020: 'Yan Afirka masu gasar hawa sama na fatan karfafa gwiwar matasa

Dukkan matasan biyu sun zaku domin ganin wasan hawa sama ya bunkasa a nahiyar Afirka Dukkan matasan biyu sun zaku domin ganin wasan hawa sama ya bunkasa a nahiyar Afirka

'Yan wasa biyu da za su wakilci Afirka a gasar hawa sama, na fatan za su zaburar da masu sha'awar wasanni a nahiyar domin su ma nan gaba su shiga fagen a dama da su.

'Yan wasan duka 'yan Afirka ta Kudu ne, Christopher Cosser, mai shekara 20; da Erin Sterkenburg mai shekara 17, da za ta fito gasar wasannin mata.

Dukkan matasan biyu sun zaku domin ganin wasan hawa sama ya bunkasa a nahiyar Afirka, saboda baki daya mutum 22 kadai suke wannan wasa a nahiyar. Ashirin daga ciki 'yan Afirka ta Kudu ne, sai biyu daga kasar Uganda, da za su yi wasan a watan Disamba.

Tuni Cosser ya doke 'yan wasa maza 13 ida ya samu gurbin tafiya Olympic, yayin da Sterkenburg ta doke 'yan wasa mata.

Annobar korona ta sa an samu raguwar adadin 'yan wasan hawa sama inda mutum 500 ne suke fafatawa a gasar daga nahiyar Afirka.

A yanzu kasashen Algeria, da Botswana, da Kamaru, da Mauritius, da Rwanda, da Senegal, da Afurka ta Kudu da Uganda ne suka yi rijista da hukumar wasan hawa sama ta duniya.

"Ina fatan samun damar halartar gasar da zan yi, zai bunkasa wasan hawa sama a daukacin nahiyar Afurka," in ji Cosser.

"Na san ba abu ne da za a cimma nan kusa ba, amma ina fatan nan da shekara 10 za mu samu karuwar masu sha'awar wasan, mu samu yara da ke son shiga gasar, da fatan za su samu komai cikin sauki ba kuma tare da an kashe makudan kudade ba."

Ita ma Sterkenburg na fatan ganin wasan ya samu karbuwa ta yadda zai bunkasa a nahiyar.

"Yawancin mutane ba su da masaniya kan wasan hawa bango ko sama, amma bayan gasar Olympics ta bana, na san mutane da dama za su yi sha'awarsa saboda za a nuna a gidajen Talabijin."

"Daga nan sha'awar wasannin za ta bunkasa, saboda a kodayaushe burinmu shi ne mu ga sabbin mutane na shiga fagen domin a dama da su," in ji Sterkenburg.

Kamar sauran 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a fadin duniya, matasan biyu sun ci gaba da yin atisaye duk da dokokin da aka sanya na yaki da cutar korona.

Lokacin da aka sanya dokar kulle a shekarar da ta gabata a Afirka ta Kudu, Sterkenburg da Cosser, sun yi amfani da farfajiyar bayan gidansu domin motsa jiki don gudun kar su kara kiba. A yanzu da aka dage dokokin suna yin atisaye yadda ya kamata da fatan ganin mafarkinsu ya zama gaskiya.

Farawa da kuruciya

'Yan wasan biyu na da bambanci kan abin da ya ja hankalinsu suka fara wasannin tun suna kanana, yayin da Cosser ya samu sha'awar wasan ta hanyar kallon fina-finai, ita kuma Sterkenburg a makaranta ta fara.

Daya daga cikin kyaututtukan da Cosser ya samu a ranar bikin cikarsa shekara 12, shi ne fim din da ya yi duba kan rayuwar wasu mutane masu hawa sama, da yadda suka dage domin cimma burinsu.

Duk da fim din minti 90 ne kacal, amma ya zaburar da Cosser domin ganin ya zama dan wasan da zai wakilci Afirka ta Kudu a gaba.

"Zan iya tuna lokacin da nake kallon kwararrun masu hawa tsauni a cikin fina-finai ko ana hira da su, sai na ce wa kai na ya kamata ni ma fa na gwada sa'a ta," in ji Cosser a hirarsa da sashen wasannin Afirka na BBC.

Bayan shafe kusan shekaru 10, ya na fadi tashi a karshe kwalliya ta biya kudin sabulu, inda dan shekara 20 din ke gab da kafa tarihi.

Saboda tsaikon da aka samu na fara wasannin Olympics, sakamakon annobar korona, za a fara wasan ranar 23 ga watan Yuli mai zuwa, Cosser zai yi amo cikin masu hawa tsauni 40 za su fafata a gasar ta bana.

"Na shiga wani yanayi na farin ciki a lokacin da sunayen wadanda suka yi nasarar shiga wasan ya fito, na kuma ga ina daya daga cikinsu," ya bayyana haka daga birnin Johannesburg.

"Ina cike da doki, ba wai kawai na wakiltar nahiyata ba, a'a sai domin cikar burina. Sabon wasa ne, kuma kasancewa cikin masu abin alfahari ne."

Kamar sauran abokan karatunta, ta fara wasanni lokacin da take aji biyu na matakin Sakandare, hawa tsauni ko bango daya ne daga cikin burinta.

"A duk lokacin da ake yi wasan, muna yawan kallon gasar Olympics tare da 'yan gidanmu, domin haka gani na a matsayin ba karamin farin ciki ya sanya ni ba," kamar yadda Sterkenburg ta shaida wa sashen wasanni na BBC.

"Ina cike da farin cikin zama a masaukin 'yan wasa na Olympic village - ina alfahari da hakan."

Wasu ka iya tsorata a duk wasan da ya danganci hawa sama, amma da Sterkenburg ta fara atisaye shekaru uku da suka wuce mahaifiyarta ta damu matuka.

"Mahaifina bai damu ba sosai, amma mahaifiyata ta damu, ta tambaye ni kin tabbata za ki iya, ba za ki fado daga sama ki ji ciwo ba?"

Tana son nuna fannin wasannin da ta dauka ba mai hadari ba ne, domin haka ta ci gaba da shiga gasar wasan a makaranta, sannan mahaifiyarta na yawan kallo, domin ta samu nutsuwa ta kuma saba da cewa 'yarta ba ta cikin hadari.

Sai dai Sterkenburg ta damu kan yadda hannunta ya yi kanta saboda hawa tsauni.

"Hannayena kullum na daure, saboda koda yaushe mutane na ce min hannunki ba shi da kyawun gani, amma na kan basar." Me ake nufi da wasan hawa sama?

A gasar wasannin Olympic na Tokyo, 'yan wasa zau kara ne awasa guda, wanda zai duba kwarewarsu kan fannoni uku: hawa tsauni cikin tawaga, yin jagora, da kuma hawa sama ko tsauni cikin sauri.

Nan gaba a wasannin Olympics, yawancin 'yan wasa na fatan za a bai wa kowanne dan wasa kyauta daban.

Dukkan wasannin ana yin su ne a inda aka gina.

  • Hawa da Sauri: za a gwada saurin dan wasa, a bango mai nisan mita 15 domin gamawa cikin takaitaccen lokaci, wanda ya yi da sauri cikin knkanin lokaci shi ya ke nasara. A yanzu a duniya baki daya wanda aka yi cikin sauri shi ne na sakan 5.48.


  • Hawa sama babu kariya: za a gwada karfin 'yan wasa, da yadda za su magance matsala ta hanyar yin tsanaki wajen duba wuraren da dan wasa zai sanya kafarsa, a lokacin hawa sama ko dai mita hudu. Dan wasan da ya magance matsalolin cikin sauri shi ne ya yi nasara.


  • Jagora wajen hawa sama: wannan na magana ne a kan nisan hawa, da dabara da kuma jajircewa. Igiya na taimaka wa 'yan wasa musamman idan suka hau sama mai nisan mita shida ta yadda ba za su fado ba. Duk dan wasan da ya fi kowa zuwa kololuwar sama shi ne ya yi nasara.