You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826954

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

Tinubu ya naɗa Badaru ministan tsaro, Wike ministan Abuja

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa tsohon Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru ministan tsaron ƙasar.

Kazalika, tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ne zai taimaka masa a matsayin ƙaramin ministan tsaro.

Tsohon Gwamnan jihar Ribas da ke kudancin ƙasar, Nyesom Wike, shi ne ministan Abuja, yayin da Maryam Mairiga daga Kano za ta yi aiki a matsayin ƙaramar ministar Abuja.

Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana sunayen ministocin da ma'aikatunsu 19 a yammacin Laraba.

Mutum 45 majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar a matsayin ministocin na Tinubu, abin da ke nufin za a sanar da sauran nan gaba. ullahi