You are here: HomeAfricaBBC2023 01 03Article 1689866

BBC Hausa of Tuesday, 3 January 2023

Source: BBC

Tennis: Raducanu da Gauff sun kai zagayen gaba a Auckland

Matashiyar yar wasan Tennis Emma Raducanu Matashiyar yar wasan Tennis Emma Raducanu

Matashiyar yar wasan Tennis Emma Raducanu ta fara shekarar 2023 da kafar dama, bayan da ta doke takwararta Linda Fruhvirtova a wasan zagayen farko na ABS Classica a birnin Aukland.

Yar Burtaniyar mai shekaru 20, ta lashe wasan 4-6, 6-4, da kuma 6-2 a kan yar kasar Czech din.

Emma Raducanu ce ta lashe gasar US Open a 2021, kuma tun a lokacin ne sunanta ya fito a duniyar Tennis.

Raducanu ta samu rauni a watan Oktoban bara, wanda hakan yasa ta dauki hutu daga wasa kafin daga baya ta dawo fagen daga.

A yanzu za ta kara da Viktoria Kuzmova yar kasar Slovakia wadda ke matsayin na 105.

Itama matashiya Coco Gauff yar kasar Amurka ta kai zagaye na gaba, bayan da ta doke Tatjana Maria yar kasar Jamus.

A daya wasan yar kasar China Zheng Qinwen ta cire Anett Kontaveit yar Estonia.