You are here: HomeAfricaBBC2023 10 25Article 1869044

BBC Hausa of Wednesday, 25 October 2023

Source: BBC

Ten Hag ya yi bayani kan wasan da zai fuskanci Copenhagen

Erik ten Hag, kocin Manchester United tare da wani dan wasa Erik ten Hag, kocin Manchester United tare da wani dan wasa

Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya yi jawabi kan wasan Champions League da zai kara da FC Copenhagen ranar Talata.

Har yanzu United ba ta ci wasa a karawa biyu da ta buga a rukunin farko ba, inda ba ta da maki ko daya.

United din ta yi rashin nasara a gidan Bayern Munich da wanda Galatasaray ta doke ta a Old Trafford.

Ƙungiyar Old Trafford, wadda take zaman makokin mutuwar Bobby Charlton, na sa ran Sergio Requilon zai buga gumurzun.

Requilon ya yi atisaye tun daga makon jiya, wanda aka sa ran zai yi wasan Premier League da United ta ci Sheffield United ranar Asabar, sai ya kamu da rashin lafiya.

A rashin Requilon da Tyrell Malacia da Luke Shaw lokacin da suka yi jinya, United ta yi amfani da Sofyan Amrabat da kuma Victor Lindelof.

Koda yake Raphael Varane ya shiga wasan da United ta buga a Premier League daga baya, amma Jonny Evans ya ji rauni a karawar.

Har yanzu mai tsaron baya, Malacia da Shaw da kuma Lisandro Martinez na jinya har da Amad.

Shi kuwa Casemiro an dakatar da shi ne daga wannan karawar yayin da yake murmurewa daga raunin da ya samu a wasan da ya bugawa Brazil.

Wannan shi ne karo na huɗu da za su kece raini a tsakaninsu, inda United ta yi nasara sau biyu, FC Copenhagen ta ci wasa ɗaya.

Wasa da aka yi tsakanin Manchester United da FC Copenhagen:

Europa League Litinin 10 ga watan Agustan 2020


  • Man Utd 1 - 0 FC Copenhagen

Champions League We 01Nov 2006


  • FC Copenhagen 1 - 0 Man Utd

Champions League Tu 17Oct 2006


  • Man Utd 3 - 0 FC Copenhagen