You are here: HomeAfricaBBC2023 01 03Article 1689881

BBC Hausa of Tuesday, 3 January 2023

Source: BBC

Tarzoma ta ɓarke a Indiya kan kisan cin zarafin da aka yi wa wata matashiya

Hoton yan zanga-zanga Hoton yan zanga-zanga

Kisan walakancin da aka yi wa wata matashiya mai shekara 20 a Delhi babban birnin Indiya a ranar 1 ga watan Janairu ya girgiza ƙasar baki daya.

Kafafen yaɗa labarai na Indiya sun rawaito cewa, matashiyar wadda ƙwararriyar mai shirya bukukuwa ce ta yi hatsari ne a ranar 1 ga watan Janairu, inda babur ɗinta ya yi karo da wata mota, a kan hanyarta ta komawa gida daga aiki.

Ƴan sanda sun ce direban da ya yi karo da ita ya ci gaba da jan matashiyar a ƙasa na tsawon wasu mil da dama.

Kyamarorin tsaro da dama sun nuna yadda jikin matashiyar ya maƙale a ƙarƙashin motar da ke ɗauke da fasinjoji huɗu.

Mene ne ke faruwa a ƙasar yanzu?

Ƴan sanda sun ce sun fara bincike ne kan babur din matashiyar bayan wasu kiraye-kiraye biyu da suka samu daga mutane a safiyar Lahadi - game da wata mata da aka ga wata mota na jan babur ɗinta, kuma an ga gawarta a kan titi a arewacin Delhi.

Sun kama wanda ake zargi tare da motarsa bayan wani bincike.

An tuhumi wanda aka kama da laifin kisan kai an kuma zargi marigayiyar da yin sakaci, kamar yadda wani babban jami'in ƴan sanda, Sagar Preet Hooda ya bayyana.

Ƴan sanda sun ce wanda aka kaman ya aro babur ɗin ne daga wani abokinsa da zimmar ya yi amfani da shi na tsawon kwana biyu.

Sun ƙara da cewa wanda ake zargi ya bar gawar matashiyar a yashe a kan titi ya gudu.

Wanda ake zargi yana a hannun ƴan sanda a yanzu, sai dai har yanzu bai ce komi ba game da lamarin.

Ƴan sanda sun ce za su yi bincike kan wannan laifi da aka aikata, kuma kwararru za su auna yadda abin ya faru domin tabbar da gaskiya.

Jami'ai sun ce za su yi amfani da gwaje-gwajen da aka yi domin tabbaatar da iƙirarin wanda ake zargi da ya ce bai ji ihun wadda ya take ba, saboda sun ƙure kiɗa a cikin motar da suke.

Me ƴan uwan marigayiyar suka ce?

Ƴan uwan wadda aka kashe - sun ce ita kaɗai ce a gidansu da take samun kuɗi - sun yi iƙirarin sai da aka yi lalata da ita gabanin a kashe ta.

Mahaifyar matashiyar ta yi tambaya cewa mai ya sanya aka tsinci gawarta a tsirara, yayin da dan uwan mahaifinta ya ce "jikinta ya nuna an ci zarafinta kafin ta mutu", in ji jaridar Time India ta bayyana hakan.

A ranar Litinin, ƴan uwanta da mazauna yankin sun yi zanga-zanga a wajen ofishin ƴan sanda na Sultanpuri, suna neman a yi bincike domin nema wa marigayiyar adalci.

Koda yake ƴan sanda har yanzu ba su tabbatar da cewa an ci zarafin matashiyar ba.

Kamfanin dillancin labarai na PTI ya ambato wani jami'in ƴan sanda na cewa, "ana ta yaɗa labaran karya da na tayar da hanakali kan cewa an yi wa marigayiyar fyaɗe gabanin kashe ta".

An aika da gawar matashiyar ranar Litinin domin gudanar da bincike a asibitin Kwalejin Maulana Azad da ke Delhi.

Tuni aka kafa wani kwamitin masu bincike da za su yi bincike a kanta.

Ƴan sanda sun ce sakamakon binciken zai iya haifar da wasu sabbin tuhume-tuhume kan wanda ake zargi.

Siyasar da ke cikin mutuwarta

Lamarin kisan ya janyo ce-ce-ku-ce ta fuskar siyasa a Delhi babban birnin ƙasar.

Jam'iyyar Aam Aadmi, wadda take shugabancin Delhi, sun gudanar da zanga-zanga ta nuna ƙin jinin gwamnatin tarayya kan abin da ta kira gazawar tsaro a birnin.

AAP ba ta da abin fada kan 'yan sanda, wadanda suke karkashin ma'aikatar cikin gida.

A ranar Litinin, mambobin jam'iyyar sun gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin Laftanar VK Saxena, suna neman ya ajiye mukaminsa kan wannan batu.

Gwamnatin Tarayya ce ta naɗa gwamnan na Delhi.

Da yake tattaunawa da kafafen yaɗa labaru, mai magana da yawun AAP Saurabh Bhardwaj ya zargi daya daga cikin mutum biyar da ake zargi cewa daya ne daga cikin mambobin BJP ya kuma zargi 'yan sandan Saxena da boye bayanai kan lamarin."

Ministan cikin gida Amit Shah bai mayar da martani kan sukar da AAP ta yi ba, amma an ruwaito cewar ya bai wa kwamishinan 'yan sanda na birnin umurnin gudanar da bincike kan lamari.

Shi ma Sexane ya ce shi ne yake lura da binciken da ake gudanarwa kan kisan.