You are here: HomeAfricaBBC2021 04 05Article 1224121

BBC Hausa of Monday, 5 April 2021

Source: bbc.com

Tarihin gicciye Yesu a mahangar addinin Kirista

Mabiya adiinin Kirisita a fadin duniya kan gudanar da bukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.

Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na Alhamis zuwa washe garin Juma'a su kuma kammala a ranar Litinin ta gaba.

A tattaunawarsa da BBC, Rabaran Murtala Mati Dangora, mataimakin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kano ya ce bukukuwan Easter sun kasu kashi biyu; akwai wanda ake kira Juma'a mai Tsarki wato ''Good Friday'', da kuma Easter Monday.

Reverend Dangora ya kara da cewa "Juma'a mai Tsarki ko kuma ''Good Friday'' rana ce ta saduda, rana ce ta komawa ga Allah, rana ce ta tunani domin wahala da Yesu Almasihu ya sha a ranar."

"A ranar ne aka zartar masa da hukuncin kisa a bisa umarnin sarkin Pontius Bilatus a wancan zamani, a ranar ne sojojin Romawa suka gicciye shi, a ranar ne kuma ya mutu, a ranar ne kuma aka saka shi a kabari bayan da aka yi jana'izarsa," in ji shi.

Ya kuma ce: ''Abin da aka bayyana a cikin littafin tsohon alkawari, cewa ya auku ne a rana ta uku da binne shi, bayan da Romawan suka gicciye shi a wani waje da ake kira Calvary ko kuma Golgotha da ke wajen birnin Kudus.''

Don haka in ji Reverend Dangora wannan rana ba ta shagali ba ce kawai, rana ce da ake son duk mabiya addinin Kirsita su yi wannan biki cikin neman salama.

''Duk lokacin da ranar Juma'a mai Tsarki ta kewayo mu kan yi kira ga jama'a da su kasance cikin saduda, da komawa ga Allah, su zama ga tunanin cewa rai mai mutuwa ne, ko wane mai rai zai dandana mutuwa, don idan har Almasihu ya mutu ba wani mahaluki da ba zai mutu ba."

Yadda aka gicciye Yesu Almasihu

Rabaran Dangora ya dada yi wa BBC karin bayani game da tarihin yadda aka gicciye Yesu Almasihu da cewa daya daga cikin almajiransa da ake kira Yahuza shi ne ya ci amanarsa ya bayar da shi ga abokan gabansa.

''An fara wannan tun ranar Laraba zuwa Alhamis, har ya zuwa ranar Juma'a da aka zarta masa da hukunci, irin yadda Romawa ke yi wa wadanda suka aikata laifi,'' a cewarsa.

Ya kara da cewa ; ''Koda yake Yesu Almasihu ba wai ya aikata laifi ba ne amma ya dauki zunubanmu ne shi ya sa ya zama kamar laifi a gare shi, don haka sai aka saka ita ce a kafa masa kusa a hannuwa da kafa aka daga shi sama.''

Wannan gicciyewar da aka yi masa a cewar malamin na Kirista, sai da ya shafe sa'oi uku zuwa hudu a kan gicciyen sannan aka bayyana cewa ya mutu, daga nan ne a cikin almajiransa akwai wani da ake kira Yusuf ya je ya roki alfarma wurin sarki cewa yana bukatar gangar jikin Yesu Almasihu zai yi masa jana'iza.

''Yadda Yahudawa suke jana'iza ya bambanta da yadda mu muke yi, yayin da muke haka rami mu saka mutum, su kuma ko wane magidanci kan tanadi rami na saka duk wanda ya rasu, don haka dama Yesu Almasihu ya riga ya tanadi wannan rami da aka saka shi aka rufe, sannna aka saka masa hatimin hukuma.''

Malam Dangora ya ce saboda farkon kafa addinin Kirista ne don haka mabiya addinin ba su dauke shi da sauki ba, sun shiga damuwa sosai don lokacin da aka zo za a kama Yesu Almasihu daya daga cikin almajiransa Bitrus ya zaro takobi ya sari wani har ya cire masa kunne.

''Yesu Almasihu ya ce, masa a'a Bitrus idan ina so za iya umartar rundunar mala'iku su je su hallaka su amma yaki ba na nama da jini ba ne, don haka ka mayar da takobinka, don haka kashe shi ya zama cikar annabci ne,'' ya ce.

Rabaran din ya kuma bayyana yadda mabiyan ke muhimmantar da wannan rana wajen yanka rago da zubar da jini wanda ke misalta Yesu don tunawa da 'yanci daga zunubi.

Ya kuma ce mabiyan kan bayar da kyaututtuka lokacin bikin Easter, in da ya ce kamar yadda aka saba a ko wane lokaci irin wannan yana yin kira ga mabiya addinin Kirista da su koma ga Allah su kuma rika yin azumi da neman tuba tare da yin la'akari da gudanar da harkokin rayuwa a kan tafarkin da Yesu Almasihu ya bar musu.

Join our Newsletter