You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816589

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Takunkumin da Ecowas ta saka wa Nijar ya fara haifar da tsadar rayuwa

Hoton alama Hoton alama

Mazauna sassan Jamhuriyar Nijar sun fara kokawa game da tsadar rayuwa da suka shiga sakamakon rufe iyakokin ƙasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Wasu 'yan kasar musamman 'yan kasuwa sun ƙara farashi kan kayayyakin masarufi, suna masu alaƙanta hakan da fara aiwatar da takunkuman da aka saka wa ƙasar sakamakon juyin mulkin na ranar Laraba.

Lamarin na faruwa ne yayin da mambobin ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma suka fara aiwatar da takunkumin daina hulɗar kasuwanci da Nijar.

Ƙasar Benin wadda maƙwabciyar Nijar ce ta ɓangaren arewaci ta rufe iyakarta.

Da ma tuni sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum suka sanar da rufe iyakokin ƙasar ta ruwa da sama da kuma ƙasa 'yan awanni bayan juyin mulkin.

Baya ga takunkuman da ta saka wa Nijar ɗin, Ecowas ta kuma bai wa sojojin ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani mako ɗaya don su mayar da Bazoum kan mulki.

Cikin matakan da ƙungiyar ta yi barazanar ɗauka har da na ƙarfin soja yayin taron da ta gudanar a Abuja ranar Lahadi.

A ranar Juma'a ne Janar Tchiani ya bayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa bayan rundunar da yake jagoranta ta dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa ta kifar da gwamnatin farar hula ta farko da ta karɓi mulki daga irinta a Nijar.

Tuni kayan masarufi suka fara yin tashin gwauron-zabi a Yamai babban birnin ƙasar, a cewar wakiliyar BBC Hausa Tchima Ila Issoufou.

Manyan motoci sun maƙale a kan iyaka

Ƙasar Benin babbar abokiyar hulɗar ce ga Nijar ta fuskar kasuwanci, inda ake shiga da motoci da kayan abinci da magunguna daga cikin ƙasar.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa wakiliyar BBC Tchima Ila Issoufou cewa akwai manyan motoci ɗauke da kwantenoni a kan hanyarsu ta zuwa Nijar da ke tsaye a tashar ruwan Kwatano.

Sai dai majiyoyin sun ce mutane na shiga da fita a kan iyakar kamar yadda aka saba.

An yi ƙiyasin cewa akwai manyan motocin jigilar kaya aƙalla 1,000 da ke shiga Nijar daga Kwatano a kullum.

Buhun shinkafa mai launin ja da ake sayarwa kan jaka 12 ya tashi zuwa jaka 15. Kazalika, mai launin ruwan ɗorawa ya koma jaka 14 daga ƙasa da hakan.

'Hauhawar farashin ta zama maras kan-gado'\

Tuni wasu mazauna birnin Yamai suka ce hauhawar farashin ta fara kaiwa matakin da ba su taɓa gani ba.

Sun kuma alaƙanta lamarin da yanke alaƙa tsakanin ƙasashen Ecowas da ƙasarsu.

"Mutane da suka ji labarin rufe iyaka kawai sai suka ƙara farashi," a cewar Mamman Nuri, shugaban ƙungiyar ADDC Wadata mai yaƙi da tsadar rayuwa a birnin Yamai.

"Wannan hauhawar farashi ma ba ta da kan-gado. Misali, duk lokacin da muka shafe farashin shinkafa bai tashi ba sosai, amma sai ga shi kwatsam ta kai jaka 14 a kasuwa," kamar yadda ya bayyana.

Ya koka cewa babu hujjar yin ƙarin saboda "ba duka ƙasashe maƙwabta ne suka yanke hulɗa da Nijar ɗin ba tukunna".

A jiya Litinin sojojin da ke mulkin ƙasar sun gana da ƙungiyar 'yan kasuwar ƙasar, inda suka nemi su fara shigar da kaya ta kan iyakar Burkina Faso.

Sai dai 'yan kasuwar sun faɗa musu cewa 'yan bindiga sun mamaye sashen ta yadda ba za su iya gudanar da harkoki ba.