BBC Hausa of Friday, 28 April 2023
Source: BBC
Ɗaliban Najeriya da suka tashi daga Sudan a motocin bas-bas zuwa ƙasar Masar, sun aika saƙonnin cewa tafiyarsu ta gamu da cikas a kan hanya.
Lamarin ya faru ne lokacin da direbobin motoci guda bakwai da suka ɗauke su daga birnin Khartoum, suka buƙaci cikon kuɗaɗensu, kafin su ci gaba da tafiya.
Ɗaliban, ta hanyar saƙonnin murya da suka aika wa iyaye da sauran makusanta kuma BBC ta samu, sun ce akwai mata masu shayarwa cikinsu lokacin da motocin suka tsaya a wani wuri da ke yankin Dongola.
Dongola, shi ne babban birnin jihar Arewacin Sudan wato Northern Sudan a gaɓar Kogin Nilu, tana kumada nisan kilomita 411 daga birnin Khartoum.
Da yammacin Laraba ne sahun farko na ɗaliban Najeriya ya fara tashi a kan hanyar zuwa Aswan, tsallaken iyakar ƙasar Masar.
An ji muryar wani ɗalibi ga alama daga birnin Khartoum yana tabbatar da cewa sun samu saƙonni daga takwarorinsu da suka tashi da yammacin jiya a motoci cewa tafiyarsu ta tsaya.
Muryar ta ci gaba da cewa bayanan da suka samu, su ne kamfanonin motocin ne suka buƙaci direbobin su dakata har sai sun karɓi cikon kuɗaɗensu daga hannun mahukuntan Najeriya.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta tabbatar da aukuwar wannan lamari, sai dai ta ce zargi kamfanin sufurin da ke jigilar ɗaliban da saɓa alƙawari.
Da misalin ƙarfe 5 na yamma agogon Najeriya ne sawun farko na motocin bas-bas - waɗanda rahotanni suka ce za su tafi cikin ayari - suka tashi daga birnin Khartoum ɗauke adadin ɗaliban.
Hukumomi ba su bayyana taƙamaimai adadin ɗaliban da aka fara kwashewa daga Sudan ɗin ba.
Sai dai a cikin dare kuma, bayanai sun ce motocin bas-bas sahu na biyu shi ma ya tashi zuwa ƙasar Masar.