You are here: HomeAfricaBBC2023 10 25Article 1868996

BBC Hausa of Wednesday, 25 October 2023

Source: BBC

Ta waɗanne hanyoyi Iran za ta iya shiga yaƙin Isra'ila da Gaza?

Hoton alama Hoton alama

Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ya yi gargaɗin cewa "yankin Gabas ta Tsakiya zai rikice" idan Isra'ila ba ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a Zirin Gaza ba.

Abdullahian ya ɗora wa Amurka alhakin hakan ta hanyar bai wa Isra'ila makamai.

Yayin wani taron manema labarai a birnin Tehran, Abdullahian ya ce: "Ina gargaɗin Amurka da yarinyarta Isra'ila, idan ba su dakatar da yaƙin nan ba, da laifukan da suke aikatawa a Gaza, komai zai iya faruwa a kowane lokaci, kuma zai iya jawowa yankin ya rikice."

A 'yan kwanakin da suka wuce, an yi ta nuna fargaba game da zafafar da yaƙin ya yi tun bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba. A gefe guda kuma, Amurka na gargaɗin kare kadarorinta a yankin, har ma ta tura kayan yaƙi a jirgin ruwanta na yaƙi mafi girma a Tekun Baharrum.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya nuna "yiwuwar bazuwar yaƙin" ta ɓangaren ƙungiyoyin da Iran ke mara wa baya, kamar Hezbollah da Hamas, yana mai cewa "Amurka na ɗaukar dukkan matakan da suka dace "wajen kare Amurkawa da 'yan Isra'ila".

Sakataren Tsaro na Amurka Lloyd Austin ya faɗa ranar Lahadi cewa: "Abin da muke fuskanta shi ne haɗarin bazuwar yaƙin ta hanyar kai wa dakarunmu da 'yan ƙasa hare-hare a yankin."

A hirarsa da kafar talabijin ta ABC, Austin ya ƙara da cewa: "Duk wata ƙasar da ke neman ta shiga yaƙin nan, shawararmu gare ta ita ce kada ta soma."

Akwai manyan alamomin da ke nuna cewa Iran na ingiza ƙungiyoyinta a yankin su shiga yaƙin, a cewar mujallar Birtaniya ta The Economist.

'Shirin shiga yaƙi'

Daga ɓangaren gabas, a Syriya, Isra'ila ta kai hare-hare a birnin Damascus da filin jirgin sama na Aleppo ranar Lahadi, inda ta dakatar da aiki a filin jirgin kamar yadda hukumomin ƙasar suka bayyana.

Daga sashen yamma kuma, a Tekun Baharrum, jirgin ruwan Amurka mai ɗaukar jirage yaƙi na can yana jira da zimmar daƙile yunƙurin Iran da ƙwayenta a Lebanon da Iraƙi da Syriya da Yemen na shiga yaƙin.

Kazalika, an tura jirgin ne don ya taimaka wa Isra'ila da bayanai da kuma makamai.

A ɓangaren kudanci ma, a kan iyaka da Gaza, akwai dubun dubatar dakarun Isra'ila inda suke jiran umarnin fara kai hari ta ƙasa a cikin Zirin na Gaza.

Haka nan a kudancin, a Tekun Maliya, jirgin ruwan yaƙin Amurka na USS Carney ya tare wasu makamai masu linzami uku da jirage marasa matuƙa da ƙungiyar Huthi ta harba daga Yemen waɗanda kuma suke kan hanyarsu ta zuwa Isra'ila.

A lokaci guda kuma, Firaministan Huthi Abdulaziz bin Habtoor ya ce ba duka makaman da suka harba jirgin ruwan ya tare ba a ranar 19 ga watan Oktoba, yana cewa wasu sun "samu damar faɗawa cikin Isra'ilar".

Bugu da ƙari, a 'yan kwanakin da suka wuce an ga yadda aka kai wa sansanonin sojan ƙawancen da Amurka ke jagoranta da jirage marasa matuƙa a Gabas ta Tsakiya.

Harin na Huthi na irin yadda ƙungiyoyi masu goyon bayan Iran ke haɗa kai wajen shiga yaƙi a yankin.

Zaɓin da Iran ke da shi na shiga yaƙin

Sayed Ghoneim ƙwararre ne a fannin tsaro da ke cibiyar Nasser Higher Military Academy kuma farfesa a Royal Military Academy da ke birnin Brussels, kuma yana ganin Iran na son ta taimaka wajen ɗorawa kan nasarar da 'yan gwagwarmayar Falasɗinawa suka samu wajen matsa wa Isra'ila.

Ghoneim na ganin shugabannin Iran na son cimma wannan bauƙata ne ta hanyoyi biyu: ta farko tun ta fara aukuwa, yayin da ake jiran ta biyun ta auku.

Hanyar farko ta ƙunshi kai hare-hare masu yawa daga arewacin Lebanon don tarwatsa sassan Isra'ila da kadarorinta.

Hanya ta biyu kuma, wadda ake jiran aukuwarta, ita ce "dukkan makaman Iran da kuma ƙungiyoyin da suke mara mata baya su fantsama cikin Isra'ila don gudanar da yaƙi sari-ka-noƙe kan sojojin Isra'ila" don su rage wa dakarun ƙasar ƙarfi a yaƙin da suke yi da Hamas a Gaza ta ƙasa.

Ghoneim ya ce irin wannan yunƙuri "zai zama mai cike da tsari da kuma taka-tsantsan". Amma to ya batun dakarun Amurka?

Ghoneim na ganin Houthi za ta ci gaba da amfani da makamai masu linzami da kuma "makaman Iran a Iraƙi don farmakar dakarun Isra'ila, wanda zai sa dakarun Amurka a yankin su dinga tare makaman, kuma hakan zai gajiyar da dakarun gaba ɗaya".

'Naɗe tabarmar kunya'

Babu mamaki gwamnatin-yaƙi ta riƙon-ƙwarya a Isra'ila na nazarin martanin da ƙasashen Larabawa za su mayar.

Akwai yiwuwar ƙarin kashe-kashen da ke faruwa a Gaza ya sa Hezbollah ta mayar da martani, da kuma ƙawayen Iran, waɗanda za su ga kamar cin fuska ne idan ba su shigar wa Falasɗinawa ba," kamar yadda mujallar Economist ta bayyana.

Ƙungiyar Hezbollah za ta samu goyon baya daga Larabawa idan ta kai wa Isra'ila hari, wadda ita kuma za ta iya fara kai hare-hare idan ta lura yaƙin zai yi ƙamari, in ji mujallar ta Birtaniya.

'Yunƙurin ƙarfafa iko'

Mujallar na ganin cewa Iran na kallon wannan yunƙuri a matsayin nasara yayin da take ƙoƙarin jaddada ikonta a Gabas ta Tsakiya.

Tsawon shekaru, Iran tana bai wa ƙawayenta horo da makamai da kuɗaɗe, kamar Hamas da Hezbollah, da tunanin cewa rikici zai iya gajiyar da Isra'ila sannan kuma ya rage wa ƙasashen Larabawan yankin karsashin adawa da ita.

Ghoneim na ganin cewa har yanzu akwai yiwuwar Iran da kanta ta shiga yaƙin duk da cewa ba ta son ta shiga yaƙi kai-tsaye da Amurka "saboda Isra'ila za ta yi amfani da damar wajen ruguza duk abin da za ta iya a Iran".

Sai dai kuma ƙawayen Iran - China da Rasha - ba za su so ta shiga yaƙin ba saboda manufofin ƙashin kansu, a cewar Ghoneim.