You are here: HomeAfricaBBC2023 02 04Article 1708214

BBC Hausa of Saturday, 4 February 2023

Source: BBC

Sudan Ta Kudu: 'Mun yi tattakin kwana tara domin mu ga Fafaroma'

Hoton alama Hoton alama

Wata ƙungiyar kiristoci mabiya ɗariƙar Katolika masu ziyara sun yi tafiyar kwana tara a ƙafa ta cikin yankin da ake yaƙi a Sudan Ta Kudu domin su yi ido biyu da Fafaroma Francis a babban birnin ƙasar Juba.

“Ƙafafuna sun riƙa min zugi, amma fa ban ji wata gajiya ba. Lokacin da yaƙini ya ratsa ka, ba zaka taɓa ganin wuyar da take cikin abun ba,” in ji wata da ake kira NightRose Falea, wadda leɓenta ya bushe.

“Ai ba zan juri rashin zuwa Juba ba, mun zo nan ne domin neman tabarrakin Fafaroma. Na yi amannar da addu’ar da zai mana abubuwa za su gyaru a ƙasarmu,” ta shaida wa BBC.

Ƙarfin imani da kishin ƙasa ne ya sanya matan tattaki daga garin Rumbek mai nisan kilomita 300 daga arewa maso yammacin Juba.

Manufarsu ita ce: su samu addu’ar da Fafaroma zai yi wa matashiyar ƙasar addu’a, wadda yaƙi ya dabaibayeta tun bayan da ta samu ‘yancin kai a 2011 – wani yanayi da ya jefa miliyoyin ‘yan ƙasar cikin yanayi na ƙasƙanci ba shi da daɗin ba da labari.

“A kullum muna tafiyar awanni ne sanna mu yada zango a inda dare ya cimmana, mu nemi coci da ke kusa mu kwana ciki. Akwai gajiya amma ta fiyar ta cancanci haka,” in ji Faith Biel.

Yayin da suke cin kilomitoci a tafiyar tasu babu abin da kake gani sai kura da ta cika ayarin, saboda waƙoƙin farin ciki da suke yi suna kuma buga ƙafafunsu a ƙasa.

Duk inda suka yi sai sun ja hankalin mutanen yankin da za su ratsa. Wasu sukan taya su rawar domin ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Wasu kuma da ba su fahimci tafiyar ta su ba, sai su buɗawa matan da ke sanye da fararen kaya da ɗankwali hanya, waɗanda ke rike da hoton Fafaroma.

Kayansu sun yi datti, ƙafafunsu sun yi buɗu-buɗu sannan laɓɓansu sun bushe a cikin tafiyar da suka yi ta kwana tara, amma duk da haka rawa suke sun tsalle suna shewa domin cikar burinsu.

Jin dadi na jiransu a cocin Katolika ta St Theresa da ke Juba, inda aka haɗa musu wani ƙwarya-ƙwaryan shagali.

Wata mai ziyara, wadda ta ke zubar da hawaye lokacin da zuka isa, ta bayyana matsalar da suka shiga ta shekaru saboda yaƙin da ƙasar ta ke fama da shi.

“Lokacin da ka shaƙi yanayin mutuwa ko kuma ka ganta da ida nunka ko ka sare game da rayuwa, kai da kanka za ka nema zaman lafiya mai ɗorewa,” in ji wata mata da ba ta so a bayyana sunanta.

“Na yi asara da yawa, amma daga baya na ga abin da ake cewa soyayya kuma mun koma magana da yare ɗaya na zaman lafiya. Ina addu’ar ko bayan tafiyar Fafaroma za mu ci gaba da zama cikin haɗin kai,” in ji ta.

Coci dai wata alama ce ta zaman lafiya a wajen mafi yawan mutanen Sudan Ta Kudu. A nan ne mafi yawan waɗanda rikici ya raba da muhallansu ke fakewa.

Fafaroma zai yi kwana uku a ƙasar, kuma zai ja ragamar addu’a a ranar Lahadi.

A 2019 Fafaroma Frances ya roƙi manyan ‘yan adawar siyasar ƙasar Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar game da zaman lafiya, lokacin da suka haɗu a fadar Vatican.

Wani lamari ne da ya girgiza jama’a da yawa, koda kuwa ba za a dakatar da faɗan ba nan take.

Duk da cewa an daina wannan rikici, amma har yanzu ana fuskantar wasu ƙananan rikice-rikice na cikin gida, kwana guda gabanin zuwan Fararoma sai da aka kashe kimanin mutum 20 a wani hari.

Miliyoyin ‘yan Sudan Ta Kudu ne ke fata da addu’ar ziyarar ta Fafaroma da sauran shugabanin kirista za ta zama farko matakin zaman lafiya ga ƙasar.