You are here: HomeAfricaBBC2023 01 27Article 1703255

BBC Hausa of Friday, 27 January 2023

Source: BBC

Sporting na zawarcin Tariq Lamptey, Tottenham na son Parro, Leeds na sanya ido kan McKennie

Tariq Lamptey Tariq Lamptey

Watakil Chelsea za ta ja kafa wajen rattaba hannu kan kwantiragin dan wasan gefe na Faransa Malo Gusto, mai shekara 19, a watan Junairun nan ne shugaban Lyon Jean-Michel Aulas ke cewa ya na sa ran dan wasan ya ci gaba da kasancewa a Faransa har zuwa akalla lokacin bazara.(Football London)

Tottenham na da kwarin gwiwa kan dan wasan Sporting Lisbon kuma mai tsaron Sifaniya Pedro Porro, inda suke fatan kammala cinikin dan wasan nan da kwanaki masu zuwa, bayan tataburzar da aka sha kan batun dan wasan mai shekara 23. (90min)

Sporting ta sake tuntuba kan batun dan wasan Brighton Tariq Lamptey, mai shekara 22, domin maye gurbinsa da Porro, ya yin da Lyon ake nuna sha'awar daukar dan wasan baya na Ghana. (90min)

Everton za ta dakatar da batun farashin fam miliyan 60 kan dan wasan Ingila winger Anthony Gordon, mai shekara 21, tare da amincewa kan farashin fam miliyan 40 bayan ainahin farashin da suka taya ya sanya Newcastle janyewa (Telegraph - subscription required)

Ana sa ran Leeds za ta biya fam miliyan 25 domin dauko dan wasan Juventus kuma na tsakiyar Amirka Weston McKennie, mai shekara 24. (Sky Sports Italy)

Bournemouth na son dauko dan wasan Roma, na tsakiyar Italiya Nicolo Zaniolo, mai shekara 23, ya yin da suke zawarcin dan wasan Villarreal, sannan na gaban Villareal Nicolas Jackson, mai shekara 21.Mail)

AC Milan  na son dauko Zaniolo, sai dai ta na nuna shawa'ar dan wasan Faransa na gaban Newcastle mai shekara 25 Allan Saint-Maximin idan cikin farko bai yiwu ba. (Sky Sports Italy)

ChelseaNewcastle da Manchester United  na zawarcin dan wasan Netherlands kuma mai tsaron gidan Inter Milan Denzel Dumfries, inda Inter ke taya shi kan farashin fam miliyan 40 ga dan wasan mai shekara 26. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Mai kai harin Blackburn Rovers Ben Brereton Diaz ya amince ya shiga La Liga a bangaren Villarreal a kakar wasa mai zuwa. Dan wasan mai shekara 23 na Chile international zai kammala kwantirahinsa da Ewood Parka karshen kakar wasa. (Mail)

Southampton na duba yiwuwar dan wasan Rennes  da Ghana winger Kamaldeen Sulemana. Mai shekara 2o din na daga cikin 'yan wasan da suka taka rawa a lokacin gasar cin kofin duniya, lamarin da ya dau hankalin Premier League da Everton mai fafutukar yadda za ta kai labari. (Mail)