You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837784

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Son ya ci kwallo uku rigis karo na hudu a tarihi a Tottenham

Son (hagu) Son (hagu)

Tottenham ta je ta ragargaji Burnley da ci 5-2 a wasan mako na huɗu a gasar Premier League da suka fafata ranar Asabar a Turf Moor.

Burnley ce ta fara zura kwallo a minti na huɗu da take leda ta hannun Lyle Foster daga baya Tottenham ta farke ta hannun Heung-min Son.

Cristian Romero ya ci wa Tottenham na biyu daf da hutu, bayan da suka koma zagaye na biyu James Maddison ya ƙara, sai Heung-min Son ya zura biyu a raga na uku rigis a wasan.

Karo na hudu kenan da Son ya ci kwallo uku rigis a Premier League a kuma filaye daban-daban.

Ya fara bajintar a St Mary a karawa da Southampton a Satumbar 2020, sannan ya ci uku rigis a Villa Park a wasa da Aston Villa a Afrilun 2022.

A satumbar 2022 ya ci Leicester City kwallo uku a filin Tottenham, sannan a Turf Moor a fafatawa da Burnley a Satumbar 2023.

Daf da za a tashi Burnley ta zare daya ta hannun Josh Brownhill.

Tottenham ta haɗa maki 10 a wasa huɗu a bana ƙarƙashin sabon koci Ange Postecoglu, kenan ya yi kan-kan-kan da bajintar Harry Rednaff da Tim Sherwood da kuma Antonio Conte.

Tottenham wadda ta fara 2-2 da Brentford ta doke Manchester United 2-0 da cin Bournemouth 2-0 da caskara Burnley 5-2 a wasan mako na hudu.

Tottenham za ta karɓi bakuncin Sheffield United a wasan mako na biyar, yayin da Burnley za ta ziyarci Nottingham Forest.